23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Wata matar aure ta halaka mijinta har lahira a jihar Kebbi

LabaraiWata matar aure ta halaka mijinta har lahira a jihar Kebbi

Hukumar ƴan sandan jihar Kebbi ta cafke wata matar aure mai shekara 30 a duniya, Farida Abubakar, bisa zargin sa hannun ta a kisan mijinta, Attahiru Ibrahim Zagga. 

Shafin Linda Ikeji ya ambato kakakin hukumar, SP Nafiu Abubakar, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Juma’a 26 ga watan Agusta.

An cakawa mamacin wuƙa wacce tayi sanadiyyar rasuwar sa

Kakakin yace Attahiru Ibrahim, wanda alƙalin majistare ne a jihar Kebbi, an caka masa wuƙa har ya mutu a gidan sa dake cikin Birnin Kebbi a daren ranar Alhamis.

A ranar 25/8/2022 da misalin ƙarfe 11:40 na dare, jami’an ƴan sanda dake a Gwadangaji, sun samu bayanin cewa anji wata baƙuwar ƙara a gidan wani makwabci, mai suna Attahiru Ibrahim, na kwatas ɗin Alieru, a Birnin Kebbi, sannan kofar gidansa a kulle take. A cewar sanarwar

Bayan samun bayanan, an tura jami’an ƴan sanda cikin gaggawa zuwa gidan inda suka shiga da ƙarfin tuwo, sannan suka tsinci Attahiru Ibrahim kwance cikin jini, wanda daga baya likita ya tabbatar da rasuwar sa

Ana zargin matar auren da aikata kisan

Haka kuma, matar sa mai suna Farida Abubakar an ganta a cikin gidan. Hakan yasa ake zargin ta sannan aka cafke domin bincike kan lamarin.

A halin da ake ciki, kwamishinan ƴan sandan jihar Kebbi, CP Ahmed Magaji Kontagora, ya bayar da umurnin tura lamarin zuwa ɓangaren SCID, Birnin Kebbi, domin gudanar da sahihin bincike wurin binciko gaskiyar lamari dangane da wannan mummunan lamarin.

Wani abokin mamacin mai suna Aminu Ubandoma ya tabbatar da rasuwar sa a wani rubutu da yayi a shafin sa na Facebook.

Yadda matashi ya halaka matarsa saboda ta shanye masa Koko

A wani labarin na daban kuma wani matashi ya halaka matar sa saboda shanye masa koko.

Wani matashi mai shekaru 20 ya halaka matarsa bisa rikicin da su ka samu saboda Koko kamar yadda majiyoyi su ka tabbatar, Amihad.com ta ruwaito.

An samu labarin yadda lamarin ya faru a kauyen Kadaura da ke Karamar hukumar Rafi, inda matar ta rasa ranta bayan mijinta ya zane ta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe