An ba da rahoton cewa matar dan majalisar California Tom McClintock ta mutu bayan ta sha maganin rage kiba da ciwon suga , da sauran cututtuka, na gargajiya, in ji sabon rahoto.
Yadda aka gano mutuwar matar dan majalisar
An gano Lori McClintock din, mai shekaru 61, ta sha magani ta hanyar hada farin ganyen Mulberry, kafin rasuwarta a watan Disambar 2021 a gidan aurenta da ke arewacin California, a cewar rahoton kafar KHN.

Dalilin mutuwar da aka jera a cikin rahoton shine, rashin ruwa saboda ciwon gastroenteritis wato murdawar ciki, wanda sakamakon shan ganyen mulberry din ne ya haifar da shi. Hakan ya fito ne a wani rahoto daga gundumar Sacramento da ke dauke da kwanan watan Maris 10 amma ba a fitar da shi ga jama’a ba.
Takardu, tare da rahoton binciken gawarwaki da kuma takardar shaidar mutuwa da aka gyara, wadda ke ɗauke da asalin musabbabin mutuwar, an fara fitar da su ne a watan Yulin 2022.
Karshen sadarwa tsakanin ma’auratan
Dan majalisar na jam’iyyar Republican ya fara jin matar tasa mai shekara 61, ba ta amsa kiransa daga gidansu na Calif or niacin, tun a ranar 15 ga Disamba, 2021, bayan ya kada kuri’a a Majalisar a daren washegarin ranar da ya dawo daga Washington, D.C.
Rahoton ya ce an samu wani farin ganyen Mulberry a cikinta, bayan gudanar da binciken gawa. Har ya zuwa yanzu dai ba a bayyana musabbabin mutuwar ta ba.
Matsalar gubar abinci da magani
Mutuwar matar dan majalisar dai, tana nuni ga illolin abinci mai guba da kuma magungunan gargajiya na wata masana’antar dala biliyan 54 a Amurka, wacce masana suka ce tana buƙatar ƙarin binciken kwakwaf daga gwamnati, kamar yadda CBS News ta ruwaito.
Daniel Fabricant, shugaban Ƙungiyar Samfuran Halitta, wanda ke wakiltar masana’antar kayan abinci, yana da shakku akan ko mutuwar McClintock din ya na da alaƙa da irin kayan wannan kamfani.
Fabricant, wanda yake kula da kariyar abinci a hukumar FDA, a lokacin gwamnatin Obama, ya ce:
“Yana da cikakken hasashen cewa akwai urumin kimiyya ga wannan matsala . Ba wai kawai abin da mai binciken ya ji ba.
“Ana yawan samun akasi, na mutane da yawa suna mutuwa daga matsalar rashin ruwa, kowacce rana, kuma akwai dalilai daban-daban da kuma sababi daban-daban da suke haddasa hakan”
Fabricant ya ce abune maib kyau da mai binciken da kuma dangin suka kai rahoton mutuwarta ga FDA saboda hakan ya baiwa hukumar damar fara gudanar da bincike.
Amurka ta bindige shugaban al Qaeda Ayman Al-Zawahiri
A ranar Asabar din da ta gabata ne Amurka ta kai wani hari a jiragen yaki mara matuki in da suka kashe shugaban Al Qaeda Ayman Al-Zawahiri,a cewar shugaba Joe Biden a wani jawabi da ya yi a fadar White House a radar litinin.
CNN ta nakalto Mista Biden yana cewa “Na bada izinin a kawo karshen shi gaba daya.
Mista Zawahiri, wanda ya cika shekara 71 a duniya, ya kasance likitan kuma makusanci ga Osama bin Laden.
A cewar Mista Biden, Mista Zawahiri “yana da hannu sosai a harin 9/11, wanda harin ya jawo asarar mutane 2,977 a kasar Amurka. Shekaru da dama, ya na daga cikin wadanda suka shirya kai harin kan Amurkawa.”
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com