34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

An Kashe Sojoji 3 Da Yan Bindiga Da Dama A jihar Zamfara

LabaraiAn Kashe Sojoji 3 Da Yan Bindiga Da Dama A jihar Zamfara
Armed Bandits 1140x570 1

‘Yan bindiga a ranar Laraba sun yi wa sojoji kwanton bauna a karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara, inda suka kashe uku daga cikin su,jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun yi wa motar sojojin kwanton bauna ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta dakile hare-haren da ‘yan ta’addan suka kai a kauyukan Fanda-Haki da ‘Yar Katsina da kuma Karrakkai.
Sojojin sun sami rahoton wani hari da ‘yan bindiga ke shirin kai wa al’umomin wannan yankin inda suka tafi izuwa wurin domin dakile harin, sai dai yan ta’addan sun budewa sojojin wuta, in ji wani mazaunin garin Hussaini Ali.

Sai dai mazauna yankin sun ce sojojin sun fafata tare da kashe ‘yan bindiga da dama inda suka kara da cewa tsananin harbin da sojoji suka yi ne ya tilasta wa maharan ja da baya.

Ƴan bindiga sun sace ƴan’uwan ɗan takarar gwamnan APC a Katsina

Ƴan bindiga sun kutsa cikin garin Dutsinma, hedikwatar ƙaramar hukumar Dutsinma ta jihar Katsina, inda suka sace mutum 6.

Mafi yawa daga cikin mutum 6 da ƴan bindigan suka ɗauke ƴan’uwa ne ga wanda ya nemi takarar gwamnan jihar a inuwar jam’iyyar APC, Umar Tata.

Yadda lamarin ya auku
Wasu majiyoyi sun shaidawa jaridar Daily Trust cewa wasu daga cikin mutanen da aka sace sun je ɗaurin aure ne a wani gida kusa da na ɗan siyasar.

Haka ma wata majiya mai tushe ta bayyana cewa infomomi sun taka rawa wurin yadda aka sace mutanen.
Matar da ƴaƴan ta ne da yawa daga cikin waɗanda aka sace ƴar’uwa ce ga Umar Tata, sannan ƴan bindigan kai tsaye suka kutsa gidan suka ɗauke matan, abin akwai alamar tambaya a ciki. A cewar majiyar

Ƴan bindiga sun addabi garin Dutsinma da hare-hare
Wani mazaunin garin Dutsinma wanda ya nemi a sakaya sunan shi, yace tun da farko ƴan bindigan sun sace mutum 9 a kwatas ɗin Unguwar Kudu, amma an sako mutum uku daga baya.

Da farko sun ƙyale wata tsohuwa wacce ba zata iya tafiya ba da wani yaro wanda yake sharɓar kuka. Bayan sun cigaba da tafiya kuma suka bar wata mata wacce ta gaji matuƙa.
A cikin ƴan kwanakin nan akwai lokacin da ƴan bindiga suka dinga shigowa Dutsinma kwana huɗu a jere suna sace mutane. Lamarin sai ƙara ta’azzara yake sannan mun damu sosai. A cewar majiyar

Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, kakakin hukumar ƴan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, bai tabbatar da aukuwar lamarin ba inda yace ba a sanar da shi dangane da lamarin ba, amma yayi alƙawarin zai tuntuɓi wakilin jaridar da zarar ya samu bayani.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe