31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Walwala : Mutane suna son yiwa Najeriya hidima amma zancen gaskiya mutane a yunwace suke – Inji Sanusi

IlimiWalwala : Mutane suna son yiwa Najeriya hidima amma zancen gaskiya mutane a yunwace suke - Inji Sanusi

Tsohon Sarkin Kano mai murabus , Alhaji Muhammadu Sanusi, ya bukaci ‘yan takarar Shugabancin  kasa da su ba da fifiko ga fannin kiwon lafiya da ilimi domin bunkasa sana’o’i.

Sanusin, wanda shine tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN)  ya yi wannan kiran ne a wani taron da gidauniyar  MAMF tare da hadin gwiwar asibitin St. Nicholas da ke Legas suka shirya a ranar Laraba.

Sanusi
Mutane suna son yiwa Najeriya hidima amma zancen gaskiya mutane a yunwace suke – Inji Sanusi

Sanusi yayi kira ga yan takarar shugabancin kasa

Yayin da yake gabatar da jawabin bude taron mai taken, ‘Tsarin Kiwon Lafiyar Najeriya: A baya, Yanzu da kuma Gaba’, Sanusin ya ce tilas ne ‘yan siyasar Najeriya musamman ‘yan takarar Shugabancin kasa,  su kasance suna da kyakkyawan tsari, na inganta dukkanin sassan da suka tabarbare.

Ya ce likitoci da malamai, ba a kula da su da kyau, don haka, aka sami tabarbarewar alamura a fannonin. 

“Ilimi da lafiya sune ginshikin tattalin arziki, idan ba mu fifita wadannan bangarorin ba, to mun gama yawo. 

Yace ,yawan tabarbarewar  ya yi yawa saboda an yi almubazzaranci da rashin gudanar da kasafin kudin da aka shirya a bangarorin lafiya da ilimi.

Bai kamata ku yiwa malaman kasarku da likitoci rikon sakainar kashi ba.Wannan dalilin ne ya sa suke barin kasar da yawa. Dole ne mu gyara wannan tabarbarewa, ta hanyar mutunta bukatun malamai da ma’aikatan lafiya.

Tilas shugabanni su mutunta sana’o’i

A matsayinmu na mutane kuma musamman a matsayinmu na gwamnatoci, mun rasa mutunta sana’o’in da ya kamata a mutunta. Malamai da likitoci ba kudi suke nema ba amma yawan kudin da muke kashewa wajen horar da ‘ya’yanmu su zama Likitoci da malamai, ba za a taba samun su ba, koda mutum ya sami aiki yana daukan albashi a kasar nan,  amma duk da haka, mutane sun cancanci rayuwa mai kyau da mutuntawa.

“Mutane suna son yin hidima amma kuma suna son cin abinci . Suma mutane ne da suke da nauye-nauye a kan su,  suna so su ilmantar  da ‘ya’yansu.  Tattalin  arzikin da muke a kai tsarine na kashin dankali. Wanda yake tauye hakkin duk wani mai karamin albashi.”

Farashin kaya yana yi tashin gwauron zabi

Sanusin  ya ce, hauhawar farashin kayayyaki a kasar nan ninkawa yake yi, inda a kowace sa’a adadin yake ninka sau biyu, kuma  ba’a kara albashin likitoci da malamai ba domin n daidaita hauhawar farashin kaya yakin, wanda  shine ya ke haifar da rashin kwarin gwiwa wajen yiwa kasa hidima.

Sanusi Lamido – Shekara 40 kenan yanzu amma babu wani cigaba da aka samu a Najeriya

Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, kuma tsohon Sarkin Kano, Alhaji Muhammad Sanusi Lamido, ya bayyana cewa Najeriya ba ta samu wani cigaba ba cikin shekara 40.

Sanusi Lamido wanda yake tsohin Sarkin Kano, ya bayyana hakane a wajen bikin murnar cikar shi shekaru 60 a duniya.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe