
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Kashim Shettima, ya ce zai maida hankali wajen yaki da rashin tsaro a kasar idan aka zabi jam’iyya mai mulki a zaben shugaban kasa mai gabatowa.
ya yi bayani a taron lauyoyi
Mista Shettima, wanda ya kasance mai sharhi a taron shekara-shekara na kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) da aka kammala a ranar Litinin a Legas, ya ce shi da kansa zai jagoranci sojojin Najeriya wajen yaki da masu aikata laifuka yayin da, Bola Tinubu, zai kula da tattalin arzikin kasar.
“Ina da gogewar shekaru 18 a rikice-rikice, zan jagoranci sojoji, shugabana kasancewar sa masanin tattalin arziki ne wanda ya mayar da Legas zuwa matsayi na uku mafi girman tattalin arziki a Afirka zai maida hankali kan tattalin arziki.
“Da yardar Allah, zan gudanar da harkokin tsaro, kuma ba wai kawai kula da tsaro ba, zan tabbatar da na jagoranci sojoji wajen yaki a fadin kasar nan,” in ji shi.
Shin shugaban kasa zai iya jagorantar sojoji?
Kalaman Mista Shettima da ya ce idan aka zabe shi a matsayin babban kwamanda mataimakin shugaban kasa, rawar da tsarin mulki ya tanada na shugaban kasa ko kuma mukaddashin shugaban kasa, ya sanya ‘yan Najeriya tunanin ko zai kwacewa shugaban sa karfi.
shugaban kasa keda ikon kula da dakaru
A cewar sashe na 130(2) na kundin tsarin mulkin 1999, shugaban Najeriya shi ke da iko na musamman a matsayin babban kwamandan sojojin kasar ba mataimakinsa ba.
Baya ga Sashin da aka ambata a sama, PREMIUM TIMES za ta iya tabbatar da cewa babu wani sashe da ya baiwa mataimakin shugaban kasa ikon jagorantar runduna ta kowace siga ko girma.
wani masani ya yi bayani
Chukwunomso Ogbe, wani manazarcin siyasa kuma lauya, ya bayyana cewa bai dace ba a matsayinsa na dan takarar mataimakin shugaban ya haye kan ikon shugaban kasa.
Ya kara da cewa Shettima zai iya yin abin da ya ce ne kawai idan shugaban sa Tinubu ya mika masa mulki.
2023:Ubangiji ne kadai ya san Waye shugaban kasar Najeriya a zabe mai gabatowa -cewar Fasto Kumuyi
A ci gaba da gabatowan zaben 2023, babban malamin cocin Deeper Life Christian Ministry, Fasto William Kumuyi, ya bayyana cewa Allah ne kadai ya ke da masaniyar waye hugaban kasar Najeriya, inji rahoton The Punch. Malamin ya bayyana cewa komai yana hannun Allah game da canjin mulki a shekara mai zuwa kuma ‘yan Najeriya za su yi murna da sakamakon.
Ziyarar da ya kai yana da ga cikin ayyukan da cocin ta shirya na busharar yakin neman zabe na kwanaki shida mai taken “Crusade Global with Kumuyi”,
Ya ce: “Game da zaben shekara mai zuwa, komai yana hannun Allah. Ina so in gaya muku, babu wani abi da zai faru sai da izinin Ubangiji komai da Izinin Sa yake faruwa.
Shin za a yi zabe a shekara mai zuwa? ba za a yi zabe ba? Wa zai zama shugaban kasa? Wanene zai fito a matsayin gwamnan kowace jiha? Allah shi kadai ya bar wa kansa sanin ansan wadannan tambayoyi Abin da ya nufa shi zai faru.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com