31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Matasa sun buɗe wurin wankin mota kyauta domin tallata Peter Obi a jihar Bauchi

LabaraiMatasa sun buɗe wurin wankin mota kyauta domin tallata Peter Obi a jihar Bauchi

Wasu matasa sun buɗe wurin wankin mota na kyauta a jihar Bauchi domin wayar da kan mutane akan takarar Peter Obi.

Peter Obi na jam’iyyar Labour Party (LP) na neman shugabancin ƙasar nan a zaɓen shekarar 2023 dake tafe.

Matasan suna yin ayyukan su a ranakun Juma’a da Lahadi, ranakun da mabiya addinin Musulunci da Kiristanci ke gudanar da manyan ibadun su.

Ana tallata Peter Obi a wurin

A wurin da ake wankin motar, akwai babban allo wanda yake kira ga mutanen garin da su ƙaunaci Peter Obi wanda aka sanya domin a samu ƙarin goyon baya ga ɗan takarar shugaban ƙasan na jam’iyyar Labour Party.

Jaridar Legit.ng ta tattaro cewa matasan sun fito ne daga garin Yalwan Kagadama a cikin jihar Bauchi a yankin Arewa maso Gabas na Najeriya.

Ɗan takarar na ƙara samun karɓuwa

Takarar Peter Obi na cigaba da samun tagomashi, inda matasa da dama ke nuna goyon bayan su ga kudirin sa na neman ɗarewa kujerar shugabancin ƙasar nan a zaɓen 2023 dake tafe.

Matasa masu sana’o’i da dama sun dinga yin abubuwa kyauta domin nuna soyayyar su ga ɗan takarar wanda tauraruwar sa ke cigaba da haskawa.

Goyon bayan da Peter Obi yake samu yafi ƙarfi a yankin Kudancin Najeriya, inda yake da ɗumbin magoya baya, mafi yawa daga cikin su matasa waɗanda ke ganin shine yafi cancanta da shugabancin ƙasar nan a zaɓe mai zuwa.

Dalilan da yasa ba zan binciki gwamnatin Buhari da sauran gwamnatoci ba -Peter Obi

A wani labarin na daban kuma Peter Obi ya bayyana dalilan da suka sanya ba zai binciki gwamnatin Buhari ba waɗanda suka gabace ta idan ya hau mulki.

Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarkashin inuwar jam’iyyar Labour Party (LP), Mr. Peter Obi, ya bayyana dalilan da suka sanya ba zai bincike gwamnatocin da suka shude ba idan ya zama shugaban ƙasa a 2023.

Ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a birnin tarayya Abuja, yayin da yake amsa tambayoyi jim kaɗan bayan ya bayyana Dr. Yusuf Datti Baba-Ahmed a matsayin mataimakin sa a zaɓen 2023. 

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe