Wani sabon bincike ya bayyana yadda mutane su ke zama masu son zuciya matsawar ba sa samun isasshen bacci, Nigerian Pulse ta ruwaito.
Wasu manazarta a Jami’aar California da ke Berkeley sun aiwatar da wasu bincike kashi uku na daban-daban inda su ka gano cewa rashin bacci na sanya mutum ya rage tausayi da kuma taimakon jama’a.
Binciken ya nuna cewa mutanen da ba sa samun isasshen bacci ba sa iya bayar da sadaka da kaso 10% idan aka hada su da masu samun bacci mai yawa.
A nazarin na biyu, an gano cewa yanayin aikin kwakwalwar mutane 24 kafin yin baccin awanni 8 yana da bambanci da yadda kwakwalwarsu ke aiki bayan samun baccin.
Binciken ya nuna cewa bacci na rage son zuciya kasancewar yana taimako wurin gyara dangane da yadda mutane ke fushi ko kuma tunani.
Sannan a bangaren binciken na uku, fiye da mutane 100 da aka gwada wadanda su ka samu bacci mai kyau a kwana uku zuwa hudu sun amsa tambayoyi dangane da taimakon jama’a.
An gano cewa marasa samun isasshen bacci sun fi nuna rashin son taimakon mutane.
Meyasa gane hakan ke da muhimmanci?
Matthew Walker, wani marubuci kuma farfesa a bangaren ilimin kwakwalwa a UC Berkeley ya ce rashin bacci na janyo rashin kirki ga dan Adam sannan yana sanya wa mutum ra’ayin rashin son taimako.
Yanzu idan aka rasa masu taimako a duniyar nan, ya za a kasance kenan. Da alamu haka duniyar za ta lalace idan mutane ba su samun isasshen bacci.
Samun bacci mai yawa da dare yana bayar da nutsuwa da lafiya kuma yana gyara yanayin zamantakewa ta hanyar sanya duniyar ta zama wuri mai dadin zama.
Na tsarkake zuciyata, na yafewa duk wanda ya cutar da iyalina- Maryam Abacha
Maryam Abaca, tsohuwar matar shugaban kasar Nageriya, ta ja hankalin yan kasa da su rungumi halayyar yafiya.
A bangaren ta, Maryam ta yi bikin murnar ranar cikarta shekara 75, tace ta yafewa duk wanda ya saba wa iyalan ta.
Maryam din ta kara da cewa, Allah ya tsarkake mata zuciyar ta, saboda haka koyau ko gobe ma ta mutu.
Matar marigayi tsohon shugaban kasa na mulkin soji, Janaral Sani Abaca, wato Maryam Abaca, a ranar Asabar 2 ga watan Afirilu, tace ta yafewa duk wanda ya sabawa iyalan ta.
Maryam din, ta fadi hakan ne a wani jawabi da ta fitar, a wajen taron bikin cikarta shekara 75, kamar yadda jaridar The Sun suka ruwaito.
Tsohuwar matar shugaban kasar Nageriyar, tace duk wani radadi zata iya yafewa saboda Allah ya tsarkake mata zuciyar ta, saboda haka daga yanzu zuwa kowanne lokaci, bata fargabar mutuwa ta dauke ta. A fadar jaridar Nigerian Tribune
Ga kalaman Maryam din :
“Allah ya tsarkake mini zuciya ta, kuma har yanzu ina raye. Na gode wa Allah akan hakan. Ko yau ko gobe a shirye nake na mutu, na godewa Allah ga wannan rayuwa.
“Ga wadanda suka saba mana ko suka cutar da mu, ina amfani da wannan dama domin in ce musu mun yafe musu, ina fata zamu yafi juna, Allah ya yafe mana gabaki daya”
Haka kuma, dattijuwar mai shekaru, ta yi kira ga yan Nageriya da su rungumi halayyar yafiya ga kowa da kowa.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Source: Daily Nigerian
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com