36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Manyan dalilai 5 da ke tunzura tsofaffi yin wuff da ‘yan mata masu jini-a-jika

Mu'amalaManyan dalilai 5 da ke tunzura tsofaffi yin wuff da 'yan mata masu jini-a-jika

Ba abin mamaki bane dangane da yadda aka ga tsofaffi su na rububin mata masu kananun shekaru musamman idan aka zo batun soyayya ko auratayya, Nigerian Pulse ta ruwaito.

Akwai abubuwan da mutane su ka yarda da su a matsayin dalilan da su ka sa maza masu shekaru ke son ‘yan mata, hakan kuma na matukar sanya su nishadi da walwala.

Ga wasu daga cikin dalilan da su ke sanya maza yin hakan:

  1. Yin rayuwa babu takura da morar kudinsu

Don yin rayuwa cike da walwala, tsofaffin maza su na neman mata masu kananun shekaru kasancewar ba su da damuwa dangane da matsalolin rayuwa kuma hakan yana ba su nishadi.

Yayin da maza ke kara shekaru, su na fama da matsaloli iri-iri, hakan ke sanya su neman mafita don mantawa matsalolinsu.

  1. Ba sa son a kwaba musu

Yayin da mutane ke kara yawan shekaru, su na kara zama masu tsayayyar rayuwa da ra’ayi, ba tare da son wani abin duniya ya takura musu ba.

Maza masu shekaru su na neman mata masu karancin shekaru saboda ba sa don a dakatar da su daga yin wasu abubuwan da su ke da ra’ayin yi, ba kamar yadda mata masu shekaru su ke yi ba.

  1. Tunawa da yarintarsu

Yayin da lokaci ke kara wucewa, kowa yana so ya dinga tunawa da lokacin yarintarsa. Duk da dai shekaru na kara fadawa ko kuma lafiya tana gushewa amma mutane na neman abubuwan da za su mayar da su yara.

Don haka maza masu shekaru ke neman mata masu karancin shekaru wadanda su ke yin harkokinsu na rayuwa, yadda za su more.

  1. Gina alaka mai karfi

Sau dayawa mata masu karancin shekaru su na gina alaka mai karfi, tare da jajircewa wurin gina rayuwa, yayin da maza masu karancin shekaru ke kokarin neman na kansu.

Maza masu shekaru na fahimtar cewa dama tsawon shekarun da su ka yi a baya sun kwashe su tare da iyalansu. Samun mace mai karancin shekaru yana taimaka wa tsoho wurin more tsufarsa.

  1. Harkar kwanciyar aure

Maza masu shekaru sun fahimci cewa mace mai kananun shekaru ta ci dadin kwanciya. Kuma sun fi morewa wurin yin hakan maimakon matansu masu shekaru masu yawa.

Wata budurwa ‘yar shekara 15 ta yiwa kanta allurar jinin masoyin ta mai dauke da cutar kanjamau domin kada a raba su

Wata budurwa ‘yar shekara 15 a yankin  Sualkuchi, da ke birnin Assam na kasar Indiya ta yi wa kanta allurar jinin da ke dauke da cutar kanjamau na saurayinta, a jikinta bisa dalilin zurfafawa, gami da nunasoyayyar gaskiya a gareshi  .

Yadda budurwar ta hadu da masoyin nata

Rahotanni sun bayyana cewa,  matashiyar ta hadu da saurayin nata ne ta hanyar Facebook. Daga nan sai  ƙaunar  juna ta ƙaru a tsakanin su, a sakamakon hirar da suke yi akai-akai wadda ta sanya suka kara shakuwa, ta yadda suke jin cewa daya bazai iya rayuwa ba idan babu daya. 

A cewar gidan talabijin na Kalinga, masoyan sun kasance tare tsawon shekaru uku da suka wuce kafin yarinyar ta dauki wannan matsanancin  matakin. 

A can baya budurwar tayi yunkurin guduwa da saurayin

An ruwaito cewa, yarinyar ta kuma yi kokarin guduwa da masoyinta sau da dama a baya,  amma iyayenta  suna dawo da ita gida.Amma wannan danyen aiki da budurwar ta yi a wannan karon sam babu wani daga yan uwan ta ko kewaye da ya taba tsammanin kasancewar sa.

Ta yiwa kanta allurar jini mai cutar kanjamau

 Yarinyar ta yi wa kanta allurar jinin da aka dauka daga wurin masoyinta mai cutar kanjamau, ta hanyar amfani da sirinji.Bayan yan uwanta  sun sami labarin wannan lamari mai ban mamaki, sai suka yi karar  masoyin nata a gaban shari’a . 

Yanzu haka ‘yan sanda sun tsare saurayin nata,  yayin da ita kuma take  karkashin kulawar likitoci

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe