Wani ango ya tarwatsa auren sa ta hanyar nuna cin amanar da amaryar sa tayi ana tsaka da ɗaurin auren su. A cikin bidiyon masoyan biyu na shirin ɗaukar rantsuwar aure, sai faston dake ɗaura auren ya tambayi ko akwai wanda yake adawa da auren na su.
Cikin mamaki kawai sai angon ya ɗaga hannun sa, hakan ya bar mutanen wurin cikin kaɗuwa da mamakin abinda zai faɗa. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Angon ya fasa ƙwai
Angon ya fuskanci amaryar sannan ya bayyana yadda yake matuƙar son ta. Yace mata yana da wani abu a ran sa da yake son faɗa mata amma bai san ta yadda zai gaya mata ba. A cewar sa, hakan yasa ya yanke shawarar ya nuna mata komai a cikin faifan bidiyo a ranar auren su.
Bayan ya kammala magana da amaryar, sai ya ɗauko abin kunna talabijin ya kunna bidiyon ga mutanen da suka halarci ɗaurin auren.
Bidiyon ya nuna amaryar na sumbatar wani mutum na daban, hakan ya sanya kowa yin ihu cikin kaɗuwa. Amaryar taji matuƙar kunya inda ta rufe fuskarta da filawar dake hannun ta.
Ga bidiyon nan ƙasa:
Mutane sun tofa albarkacin bakin su
Victorfash ya rubuta:
Na tabbata ya kunna bidiyon ne a gaban mutane domin ya wanke kan shi daga zargin ya cuceta. Yanzu ya huta da yin bayanin dalilin da ya sanya ya rabu da ita. Yayi amfani da dutse ɗaya ya jefi tsuntsu biyu.
Imade_prissylaz ya rubuta:
Na san mutane da yawa za su ce mutumin mugu ne, amma meyasa za ta ci amanar sa bayan tasa zata yi aure. Idan baka son aure kayi zaman ka kawai.
Tsabar munin amarya yasa mahaifiyar ango tasa an fasa aure ana tsaka da biki
A wani labarin na daban kuma mahaifiyar ango tasa an fasa aure ana tsaka da biki.
Wani bikin aure a ƙasar Tunisia ya watse bayan uwar ango ta umurci ɗan ta ya fasa auren amaryar mai suna Lamia Al-Labawi, saboda yawan gajartar ta da muni.
Jaridar Legit.ng ta samo daga Mirror.co.uk cewa angon ya fara ganin amaryar ne a karon farko a wurin taron bikin, inda kawai hotunan ta yake gani kafin zuwan ranar bikin
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com