Jami’an ƴan sanda a jihar Ogun sun cafke wata budurwa mai shekara 23, Mary Olatayo, bisa zargin siyar da jaririnta mai sati uku a duniya kan kuɗi N600,000.
An dai cafke budurwar ne bayan da mahaifin jaririn ya shigar da ƙorafi a ofishin ƴan sanda na Mowe a ƙaramar hukumar Obafemi-Owode ta jihar Ogun.
Jaridar Daily Trust ta ambato kakakin hukumar ƴan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.
Budurwar na soyayya da mahaifin jaririn
Mahaifin jaririn ya gayawa ƴan sanda cewa soyayya suke yi da budurwar sannan sai ta samu cikin sa.
A cewar sa, mahaifin jaririn yace ya kama mata gidan haya inda ta rayu har zuwa lokacin da ta haifi jaririn.
Shi (mahaifin jaririn) ya kuma ƙara ƙorafin cewa budurwar tayi ɓatan dabo da jaririn daga gidan hayan sati uku bayan ta haihu. Inda aka gano ta a wani otal tare da wani mutum suna sharholiya.
Duk ƙokarin ganin sanin inda za a gano jaririn ya ci tura. Cewar Oyeyemi
Ta amsa laifin da ake tuhumar da ta da shi
Oyeyemi yace bayan amsar ƙorafin, DPO na Mowe, SP Folake Afeniforo, ya tura jami’an sa zuwa otal ɗin inda ake cafke wacce ake zargin aka kawo ta ofishin ƴan sanda.
Yayin da take amsa tambayoyi, Mary Olatayo ta bayyana wa ƴan sanda cewa ta siyar da jaririn ne ga wani mutum a jihar Anambra kan kuɗi N600,000.
Tace ƙawarta Chioma Esther Ogbonna, itace ta haɗa da mai siyan a jihar Anambra sannan suka raba kuɗin dai-dai. A cewar sa.
Kakakin ya kuma bayyana cewa bayanan ta su suka sanya aka cafko Chioma Esther Ogbonna, wacce ita ma ta tabbatar da maganar Mary.
A cewar sa, binciken da ƴan sanda suka ƙara gudanarwa ya nuna cewa Mary Olatayo, ƴar asalin Omu-Aran a jihar Kwara, karuwa ce, wacce take ganin cewa jaririn zai kashe mata kasuwa saboda haka ta yanke shawarar siyar da shi.
Talauci ko ƙeta: Yadda aka cafke wata mata na ƙoƙarin siyar da ɗan cikinta kan kuɗi N243k
A wani labarin na daban kuma an cafke wata mata na ƙoƙarin siyar da ɗan ta kan kuɗi N243k.
An cafke wata mata bisa ƙoƙarin sayar da yaron ta mai shekara bakwai a duniya ga mutanen da bata san su ba kan kuɗi £4,000, (N243k)
Matar wacce ta haifi yara uku anyi zargin ta tallata ɗan na ta a matsayin na sayarwa a ƙoƙarin ta na biyan basussukan da ta ci.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com