34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Keken ‘yan gayu: Yadda direban Napep ya kayata Kekensa da winduna da kofofin gilas

LabaraiKeken ‘yan gayu: Yadda direban Napep ya kayata Kekensa da winduna da kofofin gilas
  • Wani direban Keke Napep a Jos, Jihar Filato ya yanke shawarar kayata sana’ar, hakan kuma ya yi matukar daukar hankalin mutane
  • Maimakon ya bar kekensa a bude kamar yadda aka saba, ya kara gilas a winduna da kuma kofofin kenan inda ta sauya kwarai
  • Hotunan keken wanda ya bazu ta ko ina ya sanya mutane yaba masa inda su ke kiransa da mutum mai fasaha ta musamman

‘Yan Najeriya da dama sun zage wurin taya wani mai kake Napep sambarka bayan ya sauya yanayin kekensa inda ta koma ta musamman, Legit.ng ta ruwaito.

Wani matashi wanda mazaunin garin Jos ne a Jihar Filato ya kara winduna da kofofin gilas a jikin kekensa, wanda hakan ya rikida keken ta koma ta ‘yan gayu.

Shin da kansa yayi?

Windunan da kofofin sun zauna kwarai a jikin keken wanda hakan ya sanya hankula su ka karkata jama’a na tu’ajjibi akan yadda yayi tsarin.

Duk da dai babu wanda zai bayyana gaskiyar bayani akan ko shi dakanshi yayi wa keken kirar ko kuma kai ta yayi wata ma’aikata don a sauya mata yanayi.

Hotunan keken ta musamman ya bazu a shafukan Facebook din mutane da dama ciki har da ‘yan Kaduna da kuma wata kungiya ta ‘yan Jos.

Ma’abota amfani da manhajar Facebook sun dinga tsokaci yayin da su ke yaba wa dabarar mutumin.

Duk da dai akwai wadanda su ka dinga kushewa har suna cewa zai janyo zafi cikin keken. Ga dai wasu daga cikin tsokacin mutane:

Akinola Yusuf Lanre Clazzone yace:

“Wannan keken ba za ta iya zama a Legas ba, don idan ta yi karko ta yi kwana biyu, wadannan mutanen marasa hakuri za su fasa ta.”

Ezeaneche Precious tace:

“Keken ta fi dacewa da wadanda za a kai gidan yari daga kotu.”

Morolake Grace Olaoluwa tace:

“Idan har wasu su na ganin kyawun wannan gilas din, ni kuma ina ganin hatsarinsa kasancewar wasu direbobin musamman na Najeriya su na tukin ganganci.”

Hotunan keke Napep mai amfani da wutar lantarki da aka ƙera a Maiduguri ya ɗauki hankula

Hotuna masu ƙayatarwa na Keke Napep (Adaidaita Sahu) da aka ƙera a Maiduguri na kamfanin Phoenix Renewable Limited, na cigaba da ɗaukar hankula a kafafen sada zumunta.

Hotunan sun ɗauki hankula

Hotunan keken mai tayoyi uku wacce akafi sani da keke Napep sun ja hankulan ƴan Najeriya, inda suka buƙaci da ta tallafawa kamfanin. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

Mamallakin kamfanin da ya ƙera keken, Mustapha Gajibo, sananne wurin ƙera motoci masu amfani da lantarki.

Sababbin keke Napep ɗin za su iya yin tafiyar kilomita 120 bayan anyi musu caji na minti 30.

Ƴan Najeriya sun tofa albarkacin bakin su

Ƴan Najeriya da dama sun garzaya wurin yin sharhi akan wallafar da akayi a shafin Facebook na Northeast Reeporteers, domin bayyana ra’ayoyin su.

Ga kaɗan daga ciki:

Akpama Obeten Enang ya rubuta:

Waye yace Najeriya ba zata dinga tsole wa sauran ƙasashe ido ba idan da zamu birne abubuwan dake rarraba mu, mu rungumi abubuwan da suka haɗa kawu nan mu.

AbdulGaneey Baba Ajia ya rubuta:

Alamar nasara domin duk bayan wani yaƙin da akayi nasara, abubuwan ƙere-ƙere na biyo baya. Jihata abin alfahari na Borno na farfaɗowa

Sampson Oluwarotimi Fabowale ya rubuta:

Fasaha mai girma. Najeriya na kan hanyar samun ɗaukaka. Jinjina ga injiniyoyin bisa  wannan dabarar ta su

Augustine Sylvester ya rubuta:

Ubangiji zai cigaba da ƙara maka ilmi idan manyan mutanen Maiduguri suka ƙi taimaka maka ka faɗaɗa ayyukan ka, ba za su iya hana Ubangiji yasa ka ɗaukaka ba

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe