
A ci gaba da gabatowan zaben 2023, babban malamin cocin Deeper Life Christian Ministry, Fasto William Kumuyi, ya bayyana cewa Allah ne kadai ya ke da masaniyar waye hugaban kasar Najeriya, inji rahoton The Punch. Malamin ya bayyana cewa komai yana hannun Allah game da canjin mulki a shekara mai zuwa kuma ‘yan Najeriya za su yi murna da sakamakon.
Ziyarar da ya kai yana da ga cikin ayyukan da cocin ta shirya na busharar yakin neman zabe na kwanaki shida mai taken “Crusade Global with Kumuyi”,
Ya ce: “Game da zaben shekara mai zuwa, komai yana hannun Allah. Ina so in gaya muku, babu wani abi da zai faru sai da izinin Ubangiji komai da Izinin Sa yake faruwa. Yana sarrafa duk abin da ke faruwa a duniya.
Shin za a yi zabe a shekara mai zuwa? ba za a yi zabe ba? Wa zai zama shugaban kasa? Wanene zai fito a matsayin gwamnan kowace jiha? Allah shi kadai ya bar wa kansa sanin ansan wadannan tambayoyi Abin da ya nufa shi zai faru.
Dattawan kabilar Ibo sun fara tuntubar Arewa domin mulki ya koma gurin su , sun gana da Sultan da sauran mutane
Dattawan Kudu-maso-Gabas da manyan ’yan siyasa sun karfafa tuntubar manyan sarakunan addini da na gargajiya don daidaita shirinsu na neman shugabancin kasa ga dan kabilar Ibo a zaben 2023.
Daga cikin wadanda aka tuntuba, akwai Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci ta Najeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar.
Sakataren kungiyar tuntuba ta dattawan kabilar Ibo yayi jawabi
Babban sakataren kungiyar tuntuba ta dattawan kablar Ibo, Farfesa Charles Nwekeaku ne ya bayyana haka a wata hira da jaridar PUNCH ta ranar Lahadi.
A cewarsa, bayan da jamiyyar PDP, ta ci amanar kabilar Igbo, sun sake ganin wata hanya ta neman shugabancin kasar a shekarar 2023, ta hannun dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, wanda ya ce yana samun goyon bayan ‘yan Arewa.
Ya ce,
Tabbas kun karanta inda (Ango) Abdullahi shugaban kungiyar dattawan Arewa ya ce ba su yarda da jam’iyyar PDP ba. Tabbas kun karanta hakan.
Mun kai gare su; har yanzu muna magana da su. Mun ziyarci Sarkin Musulmi. Har ma ina cikin tawagar da ta same shi. Don haka, ina magana ne da salo na iko.
“Kowa yana zuwa kasuwa, kuma yau kasuwa ba ta da kyau ga talakawan Najeriya , kowane mutum yana ji a jikin sa.
“Kowane dan Najeriya, wanda matsakaicin dan kasa ne mai son cigaba , to yana son canji a yau . Wannan sauyi kuwa yana tattare da goyon bayan Peter Obi na jam’iyyar Labour. Don haka kungiyar tuntuba ta dattawan Igbo tana aiki tukuru
wajen kaiwa ga cimma nasara , kuma ba wai don Obi dan Ibo ne ba.
“Mun tantance su, kuma ya sha gaban su, ta fuskar samar da canji, canjin da za’a dade ana labari. Duk sauran mutane suna ambaton kowanne ɗaya daga cikinsu, sune suka kasance a cikin gwamnati; me suka tsinanawa wani? Sune silar matsalar da muke fama da ita a yau.”
Ba yankin Ibo kadai ke da matsar rashin tsaro ba
Ya kuma ce kalubalen tsaro a yankin Kudu-maso-Gabas da ake zargin masu fafutukar kafa kasar Biafra, ba kadai yankin jihohin Ibo ke da matsalar ba.
Nwekeaku ya ce,
“Rashin tsaro ba yankin Kudu maso Gabas kadai yake ba. Zaku iya tunawa cewa ‘yan bindiga sun kai wa ayarin motocin shugaban kasa hari, kuma babu wanda ya kai ga kama wadannan barayin har yau.
“Ga kuma cewa a wasu sassan jihar Neja ‘yan ta’addan sun kafa tutocinsu a can, kuma babu wanda ya isa ya kama su ya tsare su, ko ya murkushe su ko kuma kashe su.
“Ka je jihar Katsina, ‘yan bindiga sun kwace yankunan Katsina da dama. Don haka, Kudu-maso-Gabas ba zai zama wani abu daban daga wadancan ba. Amma muna kuma tabbatar da cewa zamu yi komai domin zaman lafiya ya dawo.
.
“Zaku iya tunawa, a jajibirin zaben jihar Anambra an yi ta rade-radin cewa ba za a yi zabe ba, kungiyar IPOB da sauran kungiyoyin matasa sun yi barazana , Amma a karshe, a lokacin da muka danne su, sai da aka zo aka yi zaben. Don haka a Kudu maso Gabas za a yi zabe da yardar Allah.”
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com