
Shugaban jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) na kasa, Rufa’i Alkali, a ranar Larabar da ta gabata ya ce jam’iyyar a shirye take ta hada kai kai da wasu jam’iyyu a zaben 2023 mai zuwa.
Jigo a jam’iyyar ya yi jawabi
Mista Alkali, mai baiwa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara kan harkokin siyasa ne ya bayyana hakan a Legas a wani taron manema labarai.
A cewarsa, jam’iyyar ba ta kyamar tattaunawa don gina kasa.
“Jam’iyyun da ke son tattaunawa da jam’iyyar NNPP dole ne su yi hakan a matsayin abokan zama daya kuma dole ne mu bayyana ra’ayoyinmu kan makomar kasar nan.
“Dukkan jam’iyyu daidai suke kamar yadda doka ta tanada.
“Muna tattaunawa ne game da makomar Najeriya,” in ji Mista Alkali, tsohon sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa.
Ya soki yadda ake tafiyar da siyasa
Ya kuma yi tir da yadda ake tafiyar da tattaunawar siyasa a Najeriya, yana mai cewa bai kamata wadanda za su dawo jam’iyyar su bukaci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Kwankwaso ya janye takarar sa ya bar musu ba.
NNPP ta yi zaman tattaunawa da da jam’iyyar LP
Tattaunawar kawance tsakanin jam’iyyar NNPP da Labour ta tsawon makonni ta kasa samar da sakamako saboda kowannen su ya kai ga fitar da mataimaki.
Ya kara da cewa ya kamata jam’iyyu su amince da matakin kawance ko dai a majalisar wakilai, wakilai, dattijai, gwamna ko shugaban kasa.
“A siyasa ana magana iya aiki ne.”
Ya ce Najeriya ba za ta sake yin kuskure a 2023 ba, yana mai cewa jam’iyyar NNPP za ta bullo da sabbin dabarun gina tattalin arzikin kasa idan aka zabe shi.
Ya kara da cewa “NNPP jam’iyya ce a Najeriya da zata kawo sauyi ga al’amuran siyasar kasar.”
Ya kara da cewa jam’iyyar NNPP ta kasance jam’iyyar mafi saurin yaduwa a Najeriya kuma nan ba da dadewa ba za ta samu goyon bayan mafi yawan ‘yan Najeriya a fadin kasar.
Dattawan kabilar Ibo sun fara tuntubar Arewa domin mulki ya koma gurin su , sun gana da Sultan da sauran mutane
Dattawan Kudu-maso-Gabas da manyan ’yan siyasa sun karfafa tuntubar manyan sarakunan addini da na gargajiya don daidaita shirinsu na neman shugabancin kasa ga dan kabilar Ibo a zaben 2023.
Daga cikin wadanda aka tuntuba, akwai Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci ta Najeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar.
Sakataren kungiyar tuntuba ta dattawan kabilar Ibo yayi jawabi
Babban sakataren kungiyar tuntuba ta dattawan kablar Ibo, Farfesa Charles Nwekeaku ne ya bayyana haka a wata hira da jaridar PUNCH ta ranar Lahadi.
A cewarsa, bayan da jamiyyar PDP, ta ci amanar kabilar Igbo, sun sake ganin wata hanya ta neman shugabancin kasar a shekarar 2023, ta hannun dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, wanda ya ce yana samun goyon bayan ‘yan Arewa.
Ya ce,
“Tabbas kun karanta inda (Ango) Abdullahi shugaban kungiyar dattawan Arewa ya ce ba su yarda da jam’iyyar PDP ba. Tabbas kun karanta hakan.
Mun kai gare su; har yanzu muna magana da su. Mun ziyarci Sarkin Musulmi. Har ma ina cikin tawagar da ta same shi. Don haka, ina magana ne da salo na iko.
“Kowa yana zuwa kasuwa, kuma yau kasuwa ba ta da kyau ga talakawan Najeriya , kowane mutum yana ji a jikin sa.
“Kowane dan Najeriya, wanda matsakaicin dan kasa ne mai son cigaba , to yana son canji a yau . Wannan sauyi kuwa yana tattare da goyon bayan Peter Obi na jam’iyyar Labour. Don haka kungiyar tuntuba ta dattawan Igbo tana aiki tukuru, wajen kaiwa ga cimma nasara , kuma ba wai don Obi dan Ibo ne ba.
“Mun tantance su, kuma ya sha gaban su, ta fuskar samar da canji, canjin da za’a dade ana labari. Duk sauran mutane suna ambaton kowanne ɗaya daga cikinsu, sune suka kasance a cikin gwamnati; me suka tsinanawa wani? Sune silar matsalar da muke fama da ita a yau.”
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com