31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Maasai: Kabilar da ake tofa wa amarya ‘Miyau’ a matsayin hanyar sanya wa aurenta albarka

LabaraiAl'adaMaasai: Kabilar da ake tofa wa amarya ‘Miyau’ a matsayin hanyar sanya wa aurenta albarka

Yayin da wasu kabilun duniya ke kallon tofa miyau a matsayin hanyar rashin kunya da cin mutuncin jama’a, kabilar Maasai da ke Kenya da arewacin Tanzania na kallon hakan a matsayin hanyar mutuntawa da sanya albarka, Nigerian Pulse ta ruwaito.

Kabilar Maasai kaso 1 ce bisa 100 na mutanen Kenya da arewacin Tanzania, amma an san su da dabbaka al’adunsu tsawon lokaci wadanda su ka bambanta da na sauran jama’a.

An san su da daukar hankula, hakan ya sanya jama’a ke zuwa yankinsu don yawon bude ido, sai kuma sutturunsu na daban ne.

Su na amfani da Shuka, wani yadi mai kalar ja, tare da duwatsu masu ban sha’awa a wuya da hannayensu. Sai dai ba wannan bane abin daukar hankali face al’adarsu ta tofa miyau.

Ba kamar sauran al’adun duniya ba, Maasai ba sa jin haushi don mutum ya tofa musu miyau, a wurinsu albarka ya sanya musu tare da fatan alheri.

Misali, Maasai su na tofin miyau a hannu kafin su gaisa da jama’a a matsayin hanyar mutuntawa da kuma girmamawa, duk da ba kowa ake yi wa hakan ba.

Idan kuwa aka yi maka hakan ka tabbatar kai din mai sa’a ne kuma mai daraja.

Maasai su na tofa wa jarirai miyau don yi musu fatan tsawon rai da samun nasarorin rayuwa. Ba iyayen jariran kadai ke tofa musu miyau ba, har da sauran ‘yan uwa da abokan arziki.

Wasu sun yarda da cewa tofa wa jarirai miyau na iya wanke musu zunubbansu.

Sannan sun yarda da tofa wa amarya miyau a matsayin hanyar taya ta murna, da kuma yi mata fatan ta haihu. Don haka mahaifin amaryar yana mata tofi ne a goshi da nono, don yi mata wadannan fatan.

Kabilar Hamar: Maza na gane juriyar mata ta hanyar zuga musu bulalai yayin da matan Ke kwasar rawa ana kidi

Matan kabilar Hamar da ke Ethopia suna yin wani biki mai suna “Maza”, wanda maza za su dinga zuga musu bulalai har sai jikinsu ya dinga jini da tabbai da dama, shafin The Tribe na Facebook ya ruwaito.

Tunanin shan bakin dukan da matan su ke sha yana matukar razanar dasu. Amma duk da haka sun rungumi al’adarsu kwarai ba tare da kyalewa ba.

Ana zuga matan yayin da maza su ke dukansu da bulalen katako masu girman gaske.

Juriyar zugi da radadin yayin da su ke rawa da juyi a gaban jama’a na nuna kauna da rikon amana ga mazajensu na aure da ‘yan uwansu.

Hakan yana kara sanyawa maza da dama su dauki mace da muhimmanci ko bayan an kammala bikin.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe