Lance Kofur John Gabriel, soja mai lamba A13/69/1522, ya bayyana yadda ya yaudari Sheikh Aisami Goni Gashua, babban malami a jihar Yobe, kafin ya halaka shi.
Malamin ya rasa ransa ne bayan da sojan ya harbe shi har lahira a lokacin da ya rage masa hanya a motarsa a daren ranar Juma’a. Jaridar Daily Trust ta rahoto.
Malamin ya rage wa sojan hanya
Sheikh Aisami yana kan hanyar sa ta zuwa Gashua daga Nguru lokacin da makashin na sa wanda yana a cikin kayan gida ya roƙi da ya rage mishi hanya zuwa Jaji-Maji.
Da yake magana lokacin da ƴan sanda suka tasa ƙeyar sa a ranar Laraba, sojan wanda yake tare da bataliyar 241 Recce Model, Nguru, yace Sheikh Aisami yayi masa tambayoyi guda biyu kafin ya bindige shi.
Mun kusa isa Jaji-Maji sannan tagogin motar sa na sauke, sai na ce masa ina jin ƙara a ƙasan motar sa, sai yace yana shima yana tunanin haka sai ya tsayar da motar domin ya duba.
Bayan ya tsayar da motar a gefen titi, sai ya sauka nima sai na bi sa. Bayan ya gama dubawa sai bai ga abinda yake tunani ba
Ya bayyana tambayoyin da sheikh Aisami yayi masa
A wannan lokacin na ciro bindiga ta na sanya harsashi lokacin da yake duba motar. Da bai ga komai ba a ƙarƙashin motar sai na ce masa ya duba tayar baya, amma yana cikin ƙoƙarin yin hakan sai na nuna shi da bindiga, sai ya tambaye ni, me nayi maka?
Sai na bashi amsa da babu abinda kayi min. Sai ya ƙara tambaya ta kana son ka halaka ni ne? Sai na ce masa aa bana son na halaka ka. Sai yayi shiru sannan sai na harba bindiga domin tsoratar da shi ina tunanin zai gudu.
Amma sai ya ƙi guduwa. Sai dai yana ƙoƙarin ya shiga cikin motar kawai sai na harbe shi.
Mutane da dama daga sassan ƙasar nan sun yi tofin Allah tsine bisa halaka Sheikh Aisami, inda suka buƙaci da a gaggauta hukunta masu laifin.
An cafke sojoji 2 bisa halaka wani babban malami a jihar Yobe
A wani labarin na daban kuma an cafke sojoji biyu bisa halaka wani babban malami a jihar Yobe.
An harbe har lahira wani babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Goni Aisami Gashua, akan hanyar shi daga Kano zuwa garin su na Gashua a jihar Yobe.
Ƴan sanda da shaidun gani da ido sun tabbatar da kisan malamin.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com