An yankewa wata mata ‘yar kasar Rwanda hukuncin daurin shekaru 2 a gidan yari, inda aka kama ta da laifin sanya tufafi masu bayyana Tsiraici .
Wurin da aka kama tare da tuhumar ta da bayyana tsiraici

An kama Mugabekazi Lilliane, mai shekaru 24, inda aka tuhume ta da laifin lalata a bainar jama’a yayin da take sanye da wata rigar da ta bayyana a wurin wani shagali da wani shahararren mawakin Faransa Tayc ya yi, a Kigali a ranar 9 ga Agusta, 2022.
Bayan kama ta, an tsare ta a gidan yari yayin da take jiran sauraron makomarta a kotu.
Mai magana da yawun masu shigar da kara, Faustin Nkusi ya shaidawa kamfanin dilancin labaran AFP cewa, “ana zargin ta da aikata rashin mutunci da rashin da’a a bainar jama’a.”
Magoya bayan matar sun ji haushi amma mahukunta sun gamsu da hukuncin
Labarin kamun ya haifar da fushi daga magoya bayan matar , amma jami’an gwamnatin Rwanda ciki har da tsohon ministan shari’a Johnston Busingye, sun goyi bayan matakin.
A ranar Alhamis 18 ga watan Agusta wata kotun kasar Rwanda ta yankewa Lilliane hukuncin daurin shekaru 2 a gidan yari.
Ban damu ba don yarana sun girma sun ga hotunan tsiraicina su na yawo a soshiyal midiya, Shugatiti
Shugatiti, jarumar kasar Ghana kuma ma’abociya bayyana tsiraici ta ce bata damu ba don a biyata kudi ta yi fim tsirara, DklassGh.com ta ruwaito.
A wata tattaunawa da aka yi da ita a Asempa FM, ta ce bata damu da caccakar mutane ba a kafafen sada zumunta saboda yanayin ayyukanta.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com