34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Hotunan keke Napep mai amfani da wutar lantarki da aka ƙera a Maiduguri ya ɗauki hankula

LabaraiHotunan keke Napep mai amfani da wutar lantarki da aka ƙera a Maiduguri ya ɗauki hankula

Hotuna masu ƙayatarwa na Keke Napep (Adaidaita Sahu) da aka ƙera a Maiduguri na kamfanin Phoenix Renewable Limited, na cigaba da ɗaukar hankula a kafafen sada zumunta.

Hotunan sun ɗauki hankula

Hotunan keken mai tayoyi uku wacce akafi sani da keke Napep sun ja hankulan ƴan Najeriya, inda suka buƙaci da ta tallafawa kamfanin. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

Mamallakin kamfanin da ya ƙera keken, Mustapha Gajibo, sananne wurin ƙera motoci masu amfani da lantarki.

Sababbin keke Napep ɗin za su iya yin tafiyar kilomita 120 bayan anyi musu caji na minti 30.

Ƴan Najeriya sun tofa albarkacin bakin su

Ƴan Najeriya da dama sun garzaya wurin yin sharhi akan wallafar da akayi a shafin Facebook na Northeast Reeporteers, domin bayyana ra’ayoyin su.

Ga kaɗan daga ciki:

Akpama Obeten Enang ya rubuta:

Waye yace Najeriya ba zata dinga tsole wa sauran ƙasashe ido ba idan da zamu birne abubuwan dake rarraba mu, mu rungumi abubuwan da suka haɗa kawu nan mu.

AbdulGaneey Baba Ajia ya rubuta:

Alamar nasara domin duk bayan wani yaƙin da akayi nasara, abubuwan ƙere-ƙere na biyo baya. Jihata abin alfahari na Borno na farfaɗowa

Sampson Oluwarotimi Fabowale ya rubuta:

Fasaha mai girma. Najeriya na kan hanyar samun ɗaukaka. Jinjina ga injiniyoyin bisa  wannan dabarar ta su

Augustine Sylvester ya rubuta:

Ubangiji zai cigaba da ƙara maka ilmi idan manyan mutanen Maiduguri suka ƙi taimaka maka ka faɗaɗa ayyukan ka, ba za su iya hana Ubangiji yasa ka ɗaukaka ba

Matashin da ya bar makaranta ya kera motoci masu amfani da wutar lantarki a Maiduguri

A wani labarin na daban kuma wani matashin da ya bar makaranta ya ƙera motoci masu amfani da wutar lantarki a Maiduguri.

Wani lamari mai girman gaske yana faruwa a Maiduguri, babban birnin jihar Borno. Wani matashi ɗan shekaru 29 mai suna Mustapha Gajibo yana ƙera motoci da keke mai kafa uku masu amfani da wutar lantarki sannan yana sauya fasalin injinan motoci

Abin mamaki shine Gajibo ya bar makaranta. Ya bar jami’ar Maiduguri a shekarar 2015 bayan yakai shekara ta uku. Ya bar makarantar ne saboda an bashi General Agriculture a maimakon Electrical Engineering wanda yake matuƙar so.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe