27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Acuci mata: Amarya ta fasa aure ana tsaka da shagali bayan gano angonta na da sanko

LabaraiAcuci mata: Amarya ta fasa aure ana tsaka da shagali bayan gano angonta na da sanko

Wani labari mai cike da ban mamaki ya bayyana wani wata amarya ta shafa wa idanunta toka ta fasa auren angonta bayan ta gano cewa yana da sanko, Amihad.com ta ruwaito.

Bayan kwashe lokaci mai tsawo ana shirye-shiryen aure a kasar Indiya, amaryar ta kalli cewa ba za ta iya jure ganin kan angonta da sanko ba yasa ta fasa auren.

Dama idan aure ya matso, dayawa ana samun matsaloli, ko dai daga bangaren ango ko kuma amarya. Wani lokacin kuma daga duk bangarorin.

Lamarin ya faru ne gundumar Etawah da ke birnin Kanpur cikin Jihar Uttar Pradesh, wanda sankon ango ya zama sanadiyyar fasa auren.

Jaridar Times of India ta bayyana yadda hankali kwance ake tsare-tsaren yadda za a gudanar da bikin har ta kai ga ma’auratan sun yi musayar furanni.

An samu tangarda ne bayan amaryar ta kula da cewa angon ya yi nadin gargajiya akansa ne musamman don ya boye sankon da ke kansa.

Take a wurin ta bukaci wasu daga cikin tawagarta da su taimaka su bincika mata gaskiya idan sumar bogi ce a kansa ko kuma ta gaskiya.

Bayan gaskiya ta bayyana, amaryar ta shiga tashin hankali mara misaltuwa. Ta tambayi angon dakanta don sanin gaskiyar lamarin, amma ya bayyana mata cewa dagaske sanko ne akansa.

Take anan ta fadi ta suma. Bayan dawowa daga hayyacinta, amaryar ta tsere inda ta ki amincewa a ci gaba da shagalin biki tare da ita.

Ta sanar da danginta cewa ba ta son auren mai sanko, kuma angonta yana da shi, ta fasa aurensa.

Babu yadda ba a yi da ita ba, amma ta murje idonta ta ce ba za ta taba yarda ta zauna da mai sanko ba. Danginta sun yi kokarin lallashinta amma abin ya ci tura.

Nan da nan magana ta karade ko ina, dangin mijin su ka dinga cece-kuce inda har wasu ke kallon kamar dama can yaudararsa ta yi.

Dattawan kauyen sun shiga lamarin inda su ka sasanta ta hanyar rarrashin dangin ango akan su hakura, nan da nan kowa ya watse.

Kamar yadda rahoton ‘yan sanda ya bayyana, duk bangarori biyun sun kai korafin junayensu yayin da dangin amaryar ke cewa an yaudare su ta hanyar boye sankon angon.

Daga bisani kuma duk sun janyo korafinsu inda su ka sasanta junayensu kowa ya kama gabansa.

Tsabar munin amarya yasa mahaifiyar ango tasa an fasa aure ana tsaka da biki

Wani bikin aure a ƙasar Tunisia ya watse bayan uwar ango ta umurci ɗan ta ya fasa auren amaryar mai suna Lamia Al-Labawi, saboda yawan gajartar ta da muni.

Angon bai taɓa ganin amaryar ba ido da ido

Jaridar Legit.ng ta samo daga Mirror.co.uk cewa angon ya fara ganin amaryar ne a karon farko a wurin taron bikin, inda kawai hotunan ta yake gani kafin zuwan ranar bikin.

Mahaifiyar angon na ganin Lamia ido da ido sai ranta ya ɓaci. Baa bayyana sunan angon ba, sannan haka kuma baa sanar da ranar da aka shirya bikin ba.

Amaryar ta kaɗu matuka kuma tayi baƙin ciki sosai

Cikin baƙin ciki Lamia ta garzaya kafar yanar gizo inda ta koks akan lamarin, tana cewa tayi mamakin matakin da mahaifiyar angon nata ta ɗauka.

Tace shirye-shiryen bikin sun ci mata kuɗi sosai. A cewar Pledge Times, Laima marainiya ce kuma sun haɗu da angon ne shekaru huɗu da suka gabata.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe