31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Kotu ta bada belin ɗan majalisar da yayi ɓatanci ga Annabi (SAW) a Indiya

LabaraiKotu ta bada belin ɗan majalisar da yayi ɓatanci ga Annabi (SAW) a Indiya

Wata kotu a birnin Hyderabad na ƙasar Indiya a ranar Talata, ta bayar da belin ɗan majalisar jam’iyyar Bharatiya Jhanati Party, BJP, T. Raja Singh, bayan da aka gurfanar da shi a gaban ta.

An dai gurfanar da ɗan majalisar ne bayan an cafke shi a ranar Talata bisa laifin yin wasu kalamai na ɓatanci akan fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW). Jaridar The Islamic Information ta rahoto.

Kotun taƙi amincewa da buƙatar ƴan sanda ta a sakaya ɗan majalisar inda tace ba a bi ƙa’ida ba wurin kama ɗan majalisar ba don haka ta bayar da umurnin sakin shi nan take.

Kalaman ɗan majalisar sun fusata musulmai

Kalaman Singh sun harzuƙa musulmai inda har ƙungiyar All India Muslim Personal Law Board, a ranar Talata ta bayyana su a matsayin kalaman rashin ladabi masu matuƙar ciwo. Inda tayi kira da gwamnati da ta tashi tsaye wurin hana aukuwar irin hakan anan gaba.

Wani bidiyo da aka saka Youtube ranar Litinin na ɗan majalisar yankin Goshamahal, ya nuna shi yana maimaita kalaman ɓatancin da kakakin jam’iyyar BJP, Nupur Sharma, tayi wacce tuni aka dakatar da ita.

Rikice-rikice sun ɓarke a sassa daban-daban na ƙasar a watan Yuni, a dalilin kalaman na Sharma. Haka kuma ƙasashen Larabawa sun yi Allah wadai da su wanda hakan ya jawo rikicin diflomasiyya. Hakan ya sanya BJP ta dakatar da ita.

Musulmai sun yi zanga-zangar nuna adawa da kalaman sa

Ƙungiyoyin musulmai da dama a Hyderabad sun yi zanga-zanga a ofisoshin ƴan sanda domin nuna adawa da bidiyon Singh, kamar yadda, The Indian Express ta rahoto.

Bayan ƴan sanda sun kama shi, an sake shi bayan kotu ta bayar da belin shi sa’o’i kaɗan da kamen na shi.

An kai hari ga fitaccen marubuci Salman Rushdie wanda yayi ɓatanci ga Annabi (SAW)

A wani labarin na daban kuma an kai hari ga Salman Rushdie fitaccen marubucin da yayi ɓatanci ga Annabi (SAW)

An kai hari ga fitaccen marubucin nan mai suna Salman Rushdie, wanda aka kwashw tsawon lokaci ana yi masa barazanar kisa bisa wani littafin sa da ya rubuta mai suna The Satanic Verses.

Jaridar BBC Hausa ta rahoto cewa an dai kai wa marubucin harin ne a yayin da yake jawabi a wani wurin taro a Jihar New York da ke Amurka.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe