
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sha alwashin bin diddigin masu kera sabuwar fasahar da ke bai wa masu motoci damar sauya lambobi ba tare da izini ba.
Mai magana da yawun rundunar, Muyiwa Adejobi, wanda ya bayyana haka a shafinsa na Twitter a ranar Talata, inda ya tofa albarkaci bakinsa ga wannan sabuwar dabarar.
‘yan Najeriya su guji wannan dabarar
Ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da wannan hanya, inda ya kara da cewa kowace mota tana da hakkin mallakar lamba daya ne kacal.
Martanin nasa ya biyo bayan wani faifan bidiyon da ya yadu a shafukan sada zumunta inda aka ga wata mota na amfani da wannan sabon salon mallakar lambar mota.
Motar mai dauke da lambar sirri hade da na fadar shugaban kasa, an gan ta tana sauya faifan lamban kai tsaye.
‘yan Najeriya sun maida martani
Tuni dai ‘yan Najeriya suka mayar da martani kan faifan bidiyon inda da dama suka yi tsokaci inda wasu ke kara nuna cewa wannan fasaha ce da bata gari ka iya amfani da ita.
A guji wannan fasahar
Da yake mayar da martani game da sabon tsarin, Mista Adejobi, wanda shi ma ya yada bidiyon, ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da fasahar, ya kara da cewa yana da hadari da kuma illa ga tsaron kasa.
Za a dau mataki
Ya ce rundunar ‘yan sandan za ta hada kai da hukumomin da abin ya shafa domin dakile wuce gona da iri da masu motoci ke yi dangane da lasisin lambar mota.
Jawabin Jami’an tsaro
“Mun ga wannan bidiyon tabbas Wannan fasaha ce mai kyau amma sai dai tana da hadari a al’amuranmu na Najeriya kuma ya kamata a yi Allah wadai da ita.
“Kowace mota a Najeriya dole ne a yi rajista kuma lamba daya kawai aka yadda ta mallaka.
“Za mu yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro da abin ya shafa a wannan fanni domin dakile yaduwa da kuma amfani da lambobi na jabu .
Hukumar NDLEA ta cafke wani basarake da miyagun ƙwayoyi a Sokoto
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi, NDLEA, reshen jihar Sokoto, ta cafke wani dillalin ƙwaya, Umar Muhammad, dagacin ƙauyen Ruga a ƙaramar hukumar Shagari.
Da yake magana da ƴan jarida a ranar Talata 23 ga watan Agusta, shugaban hukumar na jihar, Adamu Iro yace an cafke wanda ake zargin ne bayan aiki da wasu bayanan sirri da hukumar tayi. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
Hukumar ta daɗe tana sa masa ido
Mista Iro yace wanda ake zargin, wanda basarake ne, ya daɗe a cikin jerin sunayen waɗanda hukumar ke zargi.
Hukumar ta daɗe tana sa masa ido
Mista Iro yace wanda ake zargin, wanda basarake ne, ya daɗe a cikin jerin sunayen waɗanda hukumar ke zargi.
Da farko, mun kama matar shi ɗauke da miyagun ƙwayoyi, amma mun sake ta bayan bincike ya nuna ƙwayoyin na mijinta ne.
Yanzu Alhamdulillah a ranar Litinin mun samu nasarar cafke shi ɗauke da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 436.381 da kilogiram ɗaya na Diazepam a gidan shi
A cewar Mista Iro
Shugaban hukumar ya kuma ƙara da cewa tuni wanda ake zargin ya amsa laifin sa inda ya shaidawa hukumar cewa ya daɗe a cikin wannan baƙar sana’ar.
Hukumar NDLEA ta shirya tsaf wurin yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi
Mista Iro ya kuma tabbatarwa da mutane cewa hukumar NDLEA a shirye take wurin kai sumame a maɓoyar masu fasa ƙwauri da kuma tabbatar cewa an musu hukuncin da ya dace da su.
Ya kuma yi kira ga jama’ar gari da su cigaba da taimakawa hukumar wurin aikin da take na daƙile amfani da miyagun ƙwayoyi a cikin.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com