27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Wurare 8 Da Mutuwa ta Haramta a Duniya

IlimiWurare 8 Da Mutuwa ta Haramta a Duniya
Kotu ta daure matashin da ya gannara wa dan shekara 8 cizo a kirji

Mutane za suyi matukar mamakin yadda za a ce akwai wuraren da mutuwa ta haramta a fadin duniya.Jaridar Today Post ta yi cikakken bincike kan wuraren da sukayi jan kunne ga mutanen su da kada su sake su yi ciwo balle ta kai su ga mutuwa.

To shin mutuwar zata iya haramtuwa?

Wannan magana akwai ja a cikin ta domin kuwa hakan ba mai yiwuwa ba ne.

JERIN SUNAYEN WURAREN DA MUTUWA TA HARAMTA

1.COGNAUX,FARANSA

Wani yanki ne a Arewa maso yammacin Faransa,inda magajin garin ya haramta mutuwa a shekarar 2007 saboda an hana sa izinin bude sabuwar makabarta,sai dai daga baya hukuma ta yarje masa da yin hakan.

2.SELIA,ITALIYA

A shekarar 2015 ne Selia ta hana ‘yan kasar ta ko rashin lafiya.An yi haka ne domin ganin an magance rashin raguwar mutane a yankin shine yasa aka gargade su da kada su yadda su mutu,su cigaba da rayuwa cikin koshin lafiya.

3.SAPOURENX FARANSA

A shekarar 2008 magajin garin ya gargadi mutanen yankin da kada su sake su mutu har sai sun mallaki fegin da za a birne su saboda tsabar chunkoso da ke makabartar.

4.LONGYEARBYEN,NORWAY

Mutuwa da binnewa a yankin LongyearByen ya dade da zama haramtaccen abu tun shekarar 1950,yankin ya kasance yanada yanayi mai sanyi,kasancewar yana kusa da sashen Arctic.Ya kasance ana amfani da yanayin sanyin wurin wajen Adana gawarwaki amma saidai hakan na zame musu illa ga lafiyar mutanen yankin,shiyasa duk wanda ya zo gargarar mutuwa a wannan yanki ake kaishi wasu sassan Kasar don ya mutu a can.

5.BRITIBA MIRIM,BRAZIL

A shekarar 2005 magajin garin ya kaddamar da dokar haramtawa mazauna yankin Mutuwa a kasar,akwai tara ga mazauna yankin da sukayi taurin kan mutuwa, ko zaman gidan kaso.An halasta wannan doka ne bisa dalilin cika da makabartun wannan yanki sukayi.


6.ITSUKUSHIMA,JAPAN

Garin Itsukushima gari ne da ya kasance mai tsohon tarihi karkashin UNESCO a kasar Japan wanda aka kebe shi don bautar gumaka wanda ake kiransa da “TSIBIRI”Kasancewa wurine na tsafi da bauta,Don tsarkake wanan wuri shiyasa aka haramta mutuwa da haihuwa tun shekarar 1978,Babu asibiti ko makabarta a wannan wuri.

7.LANJARON SPAIN

A wannan yanki magajin garin ya hana mutuwa tun shekarar 1999,an kafa wannan doka ne bisa cika da makabartar wannan yanki ta yi,ana ganin cewa idan aka cigaba da mutuwa gawarwakin zasu gaza samun kwanciyar hankali a kabarurukan su.An umurci mutanen wannan yanki su kasance cikin koshin lafia har sai an yi sabon makabarta.

8.LE LAVANDOU,FRANCE

Gari ne da ya kasance a bakin Teku,a shekarar 2000 ne magajin garin ya zartar da dokan hana mutuwa a mastayin hanyar da za a bi don magance matsalar cikar makabartu.

Fasto ya mutu bayan ya sa an birne shi a kabari inda ya sha alwashin zai tashi irin yadda ‘Jesus’ yayi

Wani fasto a kasar Zambia ya mutu bayan ya yi yunkurin mutuwa kuma ya tashi kamar yadda Jesus yayi, Daily Mail ta ruwaito.

Hakan yasa yasa a daure hannayensa sannan aka birne shi a kabari na tsawon kwana uku.

Sakara, fasto ne na cocin Zion, kamar yadda rahotanni su ka bayyana, kuma kafin ya nemi a birne shi, sai da ya janyo aya daga cikin Bibul sannan ya nemi a rufe shi.

Bayan haka kabarin ne aka ga gawarsa don shirin dawowarsa da ransa bai tabbata ba.

A cikin mambobin cocin da su ka taimaka wurin rufe faston, daya ya mika kansa ga ‘yan sanda.

Har yanzu ana ci gaba da neman sauran wadanda ake zargin sun tsere.

Faston ya mutu ya bar matarsa da ciki kamar yadda rahotanni su ka nuna.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe