31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Idan mace ta cika bilicin tana rasa dandanonta a kan gado, Mr Henrie

LabaraiIdan mace ta cika bilicin tana rasa dandanonta a kan gado, Mr Henrie

Wani mai aiki a gidan rediyo, Henrie Arinaitwe wanda aka fi sani da Mr Henrie ya yi jirwaye mai kamar wanka dangane da tsohuwar budurwarsa, Prima Ndagire, yayin da ya bayyana cewa masu bilicin ba su da dadi a gado, Nigerian Pulse ta ruwaito.

Henrie ya fara soyayya da Kardash wacce ta girme shi, bayan rabuwa da George Williams Kigozi, wacce aka fi sani da Geosteady.

Ta haifi yara biyu da mawakin mai shekaru 32. Sun rabu da Geosteady ne bayan ta ki yarda ayi aurensu, auren da ta nuna kosawarta da zuwansa. Ta bayyana cewa yana ha’intarta da wasu ‘yan matan.

Baya wata daya da rabuwarsu da wani saurayin ta ne ta fara soyayya da Henrine a shekarar 2020.

A shagalin MC Richie ne ita kuma ta kulla alaka da wani mawakin Afirka ta kudu, Medi Moore. Sai lamarin yayi kama da ta bar saurayin ya a Kampala.

Bayan ta dawo Uganda su ka rabu da Henrie, inda ta bayyana hakan ta hanyar goge duk wasu hotunan da su ka dauka a shafukanta na kafafen sada zumunta.

Sai dai Mr Henrie yayin jawabi ga masoyansa a taron shagalin Rolex ya bayyana cewa:

“Amma ina karyar take? Ko karya nake yi? Duk macen da ta ciki bilicin ba ta da dadi a kan gado, haka ne koh?”

Tirkashi: Bilicin na iya janyo ciwon koda, cutar daji, hawan jini da sauran cutuka ga dan Adam, Masana

Bilicin na nufin amfani da kayyayakin da zasu haskaka wurare masu duhu a fata da kuma duk ilahirin jiki don ya yi haske.

Waɗannan kayayyakin sun haɗa da amfani da mai, sabulai, da kwayoyi, ko kuma amfani sinadarai na sulɓe fata, kamar yadda shafin Healthline.com ya nuna.

Bilicin ba ya da wani amfani

Babu wani amfanin bilicin ga lafiyar fata. Hakan baya haifar da ɗa mai ido, sannan akwai tarin matsaloli da bilicin ke haifarwa.

A lafiyance, bilicin baya da wani amfani. Amma idan ka dauki bilicin a matsayin ɗabi’arka, yana da kyau ka fahimci haɗarurrukan dake tafe dashi.

Yadda ake bilicin fata

Bilicin fata na rage yawa ko kuma samuwar sinadarin melanin a fata.

Kwayoyin halittar melanocytes ne ke da alhakin samar da sinadarin melanin.

Mutane masu duhun launin fata sun fi yawan sinadarin melanin. hasken rana da wasu kemikal na da tasiri akan samar da melalin.

Idan kayi amfani da man bilicin a fatarka, irinsu hydroquinne, su na rage yawan kwayoyin halittar melanocytes a fatarka. Wanda hakan zai yi sanadiyyar hasken fatarka.

Illolin bilicin

Ƙasashe da dama sun haramta amfani da abubuwan dake sa bilicin , saboda haɗarurrukan da ke tafe dasu.

A shekarar 2006, hukumar kula da abinci da magunguna (FDA), da sahihan majiyoyi sun fitar da sanarwa akan yadda kayayyakin bilicin ke da haɗari da tarin matsaloli.
Kayayyakin na da illa ga bil adama bisa bayyanannun hujjoji.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe