23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Saboda ba ni da kudi, sirikata ta hana matata dawowa gidana, Magidanci gaban kotu

LabaraiSaboda ba ni da kudi, sirikata ta hana matata dawowa gidana, Magidanci gaban kotu

Wani dan kasuwa mai suna Isma’il Ibrahim ya maka sirikarsa, Zainab Muhammad a wata kotun musulunci da ke Rigasa a Kaduna bisa zarginta da hana matarsa komawa gidansa, LIB ta ruwaito.

Mai karar wanda mazaunin layin da ofishin ‘yan sanda da ke Rigasa ne, ya sanar da kotu yadda sirikarsa ta dakatar da matarsa daga komawa gidansa saboda ba ya da kudi.

A cewarsa:

“Ina son matata kuma ina so ya dawo gidana, ina neman taimakon kotu akan ta dawo min da matata gidana.”

Sai dai sirikar tashi ta bayyanawa kotu cewa ta hana diyarta komawa gidan mijinta ne saboda rashin kular da mijin yake nuna mata.

A cewarta, an yi wa diyarta aiki ne sannan jaririyar ta rasu. Sai dai mijin ya kasa biyan kudin asibiti inda ya bar matar a gidan iyayenta na tsawon watanni uku ba tare da nuna kulawarsa ba.

“Ya zo bayan watanni uku da ya dawo da matarsa gida, ni kuma nace ba zan bar shi ya koma da ita ba sai bayan watanni shida, a lokacin ta warke gabadaya.

“Diyata ta yi ciwo mai tsanani bayan aikin da aka yi mata kuma ni ce na dinga biyan kudin asibiti na tsawon lokacin,” a cewarta.

Ta sanar da kotu cewa za ta yarda diyarta ta koma gidan mijinta ne matsawar ya biyata duk kudaden da ta kashe cikin watanni shidan da tayi a hannunta.

Alkalin kotun, Malam Abubakar Salis-Tureta ya dage sauraron karar zuwa ranar 4 ga watan Satumba don wacce ake karar ta kirga gabadaya kudin da ta kashe wa diyarta don mijin ya biya ta.

Sai matata ta amshi kudade masu kauri sannan take yarda mu yi kwanciyar aure, Magidanci gaban kotu

Adegbenga Dada, wanda injiniyan ruwa ne kuma dan wani basarake daga Eruku a karamar hukumar Ekiti cikin Jihar Kwara ya koka akan yadda matarsa take amshe masa kudadensa kafin ta amince dashi a shimfidar aurensu, LIB ta ruwaito.

Ya bayyana hakan ne a wata takardar kara wacce ya gabatarwa babbar kotun Kwara da ke zama a Ilorin.

Dada ya nemi a warware aurensu mai shekaru 28 da Roseline Dada akan zarginta da neman maza.

Ya zargi matarsa da kin sanin darajar kanta inda ya kara da cewa hakan ya kawo cikas ga zamantakewarsu sannan tana tura ‘yan matan wurin maza daban-daban don su amso mata kudi.

Adegbenga, wanda asalin dan Kwara ne amma mazaunin Legas ya ci gaba da cewa:

“Matata bata amsa tayin shimfidar aurena don ta koma dakin baki. Sai ta amshi kudade mai kauri sannan take amincewa ta bayar da kanta gareni. Idan har ban bata kudin ba ba za ta yarda da ni ba.

“Aurena ya lalace saboda ni da matata ba ma zama don tattaunawa akan rayuwarmu da ta yaranmu.”

Ya nemi kotu ta ba shi damar rike yaransa 3 da suka haifa.

A bangaren Roseline, ta musanta duk zargin da mijinta yayi mata inda tace shi ne manemin matan.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe