29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Hukumar NDLEA ta cafke wani basarake da miyagun ƙwayoyi a Sokoto

LabaraiHukumar NDLEA ta cafke wani basarake da miyagun ƙwayoyi a Sokoto

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi, NDLEA, reshen jihar Sokoto, ta cafke wani dillalin ƙwaya, Umar Muhammad, dagacin ƙauyen Ruga a ƙaramar hukumar Shagari.

Da yake magana da ƴan jarida a ranar Talata 23 ga watan Agusta, shugaban hukumar na jihar, Adamu Iro yace an cafke wanda ake zargin ne bayan aiki da wasu bayanan sirri da hukumar tayi. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.

Hukumar ta daɗe tana sa masa ido

Mista Iro yace wanda ake zargin, wanda basarake ne, ya daɗe a cikin jerin sunayen waɗanda hukumar ke zargi.

Da farko, mun kama matar shi ɗauke da miyagun ƙwayoyi, amma mun sake ta bayan bincike ya nuna ƙwayoyin na mijinta ne.

Yanzu Alhamdulillah a ranar Litinin mun samu nasarar cafke shi ɗauke da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 436.381 da kilogiram ɗaya na Diazepam a gidan shi

A cewar Mista Iro

Shugaban hukumar ya kuma ƙara da cewa tuni wanda ake zargin ya amsa laifin sa inda ya shaidawa hukumar cewa ya daɗe a cikin wannan baƙar sana’ar. 

Yace hukumar zata tabbatar cewa anyi binciken da ya dace cikin gaggawa akan lamarin domin miƙa wanda ake zargin kotu.

Hukumar NDLEA ta shirya tsaf wurin yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi

Mista Iro ya kuma tabbatarwa da mutane cewa hukumar NDLEA a shirye take wurin kai sumame a maɓoyar masu fasa ƙwauri da kuma tabbatar cewa an musu hukuncin da ya dace da su.

Ya kuma yi kira ga jama’ar gari da su cigaba da taimakawa hukumar wurin aikin da take na daƙile amfani da miyagun ƙwayoyi a cikin al’umma. 

Hukumar NDLEA ta ƙwace 500kg na tabar wiwi da 1kg na hodar iblis a cikin tashar mota a Kaduna

A wani labarin na daban kuma hukumar NDLEA ta ƙwace miyagun ƙwayoyi a cikin tashar mota a Kaduna.

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi  NDLEA ta ƙwace hodar iblis mai nauyin 1kg da tabar wiwi mai nauyin 511.3kg, a jihar Kaduna a ranakun Laraba da Alhamis, kwamandan sashin hukumar Umar Adoro, ya shaida wa manema labarai hakan ranar Asabar.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe