29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Daga shiga mota daya: Karuwa ta cizge kunnen matafiyi sannan ta hadiye a gabanshi

LabaraiDaga shiga mota daya: Karuwa ta cizge kunnen matafiyi sannan ta hadiye a gabanshi

Wani matafiyi ya ga takanshi bayan wata karuwa wacce tayi tatil ta giya ta cizge masa kunne sannan ta hadiye a gabansa, LIB ta ruwaito.

Kannika Kamtom, mai shekaru 25 ta tunkuri wani mai yawon bude ido mai shekaru 55 inda ta afka cikin motar hayar da yake a Thailand yayin da ta sha giya tayi tatil.

Ta tsayar da motar ne a Pattaya kafin ta kai wa matafiyin farmaki wanda ta tarar a cikin motar.

Ana zargin karuwar ta gartsa masa cizo a kunnensa na dama yayin da mutane ke wucewa a titin ranar Asabar, 20 ga watan Augusta da dare.

Yayin da yake tsaka da ihu bayan jin bakar azaba, Kamton ta yi gaggawar hadiye fatar kunnen.

Ta yi yunkurin tserewa amma kuma yadda aka yi gaggawar kiran ‘yan sanda yasa su ka yi gaggawar kama ta inda su ka sanya mata ankwa sannan ta shiga motarsu.

Nan da nan su ka zarce da ita ofishinsu.

Jami’an sun yi saurin daure kunnen mutumin wanda jini ya dinga kwarara babu kakkautawa a gefen titi sannan aka zarce da shi asibiti don samun kulawa.

Wani dan sanda mai suna Colonel Saijai Kamchula ya ce:

“Wani jami’i ne yayi gaggawar kama wacce ta kai farmakin amma sai ta kai masa duka a kafarsa. Ya yi kokarin kama ta, hakan yasa ya nemi tallafin wasu.

“Za a gurfanar da ita gaban kotu musamman don akwai shaidu da su ka ga yadda lamarin ya faru da idanunsu. Mutumin yana so a rufe matar a caji ofis sannan a hukunta ta.”

Har yanzu dai ba a san dalilin da yasa Kamton ta kai masa farmakin ba.

Bidiyon karuwa tana cin mutuncin kwastomanta akan ya ki biyanta N60,000

A wani guntun bidiyon da shafin Instablog9ja ta saki wata karuwa ta ci kwalar kwastomanta yayin da ta ce ya ki biyanta hakkintaInstablog9ja ta ruwaito.

Kamar yadda ta bayyana, ta yi masa ayyukan da ya dace ta yi masa amma ya tsere ya bar ta ba tare da biyanta ko sisi ba.-

A bidiyon wanda aka ga matar ta damki mutumin, mutane sun taru don sasanta su da jin abinda ya hada su.

Anan ne ta ke bayani kamar haka:

“Wannan mutumin ya gayyace ni, ya yi akawarin biyana N60,000. Bayan ya yi duk abinda ze yi da ni ya tsere ta katanga ya bar ni.

“Ga shi nan na kama shi. Ka biya ni kudina kawai. Ka biya ni.”

Tsokacin jama’a karkashin wallafar

Wannan bidiyon ya dauki hankalin mutane inda LabarunHausa ta tsinto wasu daga cikin tsokacin jama’a karkashin wallafar:

Mark Bosompem Wiafe ya ce:

“Yanzu mata ba su da kunya.”

Harry Peter Ugene ya ce:

“Gaskiya mutane sun haukace. Ban yarda cewa akwai masu kai wa karuwai ziyara ba sai yanzu.”

Okoye Celestine ya ce:

“In biya N60,000 ga wannan matar da ke bidiyon nan. Ubangiji ya kyauta.”

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe