34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Na shiga fim ne bayan mafalkin Fati Washa ta rike hannuna mun shiga Aljanna, Zeek Ilela

LabaraiKannywoodNa shiga fim ne bayan mafalkin Fati Washa ta rike hannuna mun shiga Aljanna, Zeek Ilela

Wani sabon jarumi a masana’antar Kannnywood, Auwal Abdullahi Zeek Ilela ya bayyana yadda yayi mafalkin cewa Jaruma Fati Washa ta rike hannunsa inda su ka shiga Aljanna a Lahira, a cewar Bashir Abdullahi El-Bash ta shafinsa na Facebook.

El-Bash wanda dama dan jarida ne ya ci gaba da bayyana yadda jarumin ya shaida cewa wannan shi ne babban dalilin da na shiga sana’ar.

Kuma a cewarsa yana fatan haduwa da Fati Washa kasancewar ya kwashe lokaci mai tsawo yana son ta.

Kamar yadda jarumin ya bayyana:

“Na dauki lokaci mai tsayi ina son Fati Washa kasancewar tana da duk wata siffa ta halittar macentaka. Wata rana na yi mafalkin mun hadu da ita a lahira, duk da dai ga ‘yan uwana da abokai da kuma sauran mutane, amma ita ce ta rike hannuna mu a shiga Aljanna tare.

“Wannan shi ne dalilin da yasa na yi shiga harkar fim don ganin mun hadu tun a duniya yadda mafalkina zai zama gaskiya a lahira.”

A cewar sabon Jarumin, mutane su na yi wa jaruman Kannywood mummunar fahimta ne, amma idan aka duba zahiri, duk mutanen kirki ne.

Don haka ya shawarci mutane da su dena musu gurguwar fahimta.

Da mutane ke bada makullin Aljanna da ba za su ba ‘yan fim ba, Hauwa Waraka

A wata tattaunawa da BBC Hausa a shirin Daga Bakin Mai Ita da suka yi a ranar Alhamis, 21 ga watan Yulin 2022, Jaruma Hauwa Waraka ta bayar da takaitaccen tarihinta.

Da farko ta fara da bayyana cewa sunanta Hauwa Abubakar amma an fi saninta da Hauwa Waraka, an haifeta a garin Jos amma a garin Kano ta girma.

Da aka tambayeta yadda aka yi ta shiga fim, ta ce da farko bata san menene fim ba ma. Akwai wasu ‘yan uwanta ne da suka kai ta Sabon Titi da ke Kano inda asalin ‘yan fim suke, daga nan ta dan fara shiga harkar jefi-jefi.

An tambayeta da fim din da ta fara, inda tace ta fara da kananu ne wadanda ba ita bace jarumar da ta haska fim din, don ko shirin Waraka wanda tayi fice dashi ba ita bace babbar jaruma a fim din.

Ta ce bayan ta dan yi fina-finai ta bar industiri na kusan shekaru 5 zuwa 7 wanda daga bisani ta dawo. Dama kuma tunda asali bata san menene fim ba dama kawai tana yi ne sama-sama.

Da aka tambayeta dalilin da yasa take fitowa a mutimiyar banza, sai tace ta san babu kyau a musulunce ayi shaye-shaye, da sauransu, amma kawai suna yi ne don fadakarwa kuma ita har yau bata shaye-shaye.

Ta ce bata jin dadin kallon da mutane suke yi mata, amma kuma tunda babu mai wuta ko Aljanna, ko kadan bata damuwa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe