- Wani guntun bidiyon da aka wallafa a TikTok ya bayyana yadda wani matashin da ake zargin dan Najeriya ne yake tallar doya a London
- A cewar mutumin, yana kokarin samun kudi ne don biyan zunzurutun haraji, hakan yasa ya ke tallar gasassar doya
- Ya bayyana yadda yayi cinikin N116,000 cikin awanni 4 bayan zuba doyar a kwalli yana tallata ta wuri-wuri
Wani dan Najeriya mai neman na kansa ya bayyana a titin London yana tallar doya kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
Wani abin burgewa shi ne yadda ba tare da Jin kunyar kowa ba ya tsaya cak a titi yana sayar da doyarsa.
Kamar yadda bidiyon ya bayyana, yana kokarin ganin ya samu karin kudi ne don biyan haraji a anguwar da yake zama a London.
Ya bayyana yadda ya kwashe awanni 4 a titi inda ya samu nasarar yin cinikin N116,000.
Ruwa ake yi gagarumi: Dan Najeriya dake tahowa daga London zuwa Legas a babur ya iso Spain
Wani mutum dan Najeriya mai suna Kunle Adeyanju ya isa ƙasar Spain a tafiyarsa ta kwanaki 25 daga birnin Landan zuwa Legas ta hanyar amfani da keken wutar lantarki Kunle ya bayyana cewa a rana ta biyu na tafiyar tasa na cike da rashin kyawun yanayi domin ana tsananin sanyi.
‘Yan Najeriya da dama da suka mayar da martani kan mukamin nasa sun yaba masa yayin da wasu ke yi masa barkwanci cewa za su so tafiya da shi idan zai koma Landan.
Wani ɗan Najeriya mai suna Kunle Adeyanju, wanda ya tashi yin tafiya mai nisa tsakanin Landan da Legas a kan babur ya ba da cikakken bayani kan tafiyar tasa.
A wani saƙon da ya wallafa a ranar Laraba, 20 ga Afrilu, mutumin ya ce ya zuwa yanzu ya yi tafiyar kilomita 720 a tafiyarsa ta kwana biyu yayin da yake tafiya daga Bourges na Faransa zuwa Girona a Spain. Mutumin ya bayyana cewa ya riga ya isa Spain.
Mutumin ya tabbata Ya bayyana cewa a rana ta biyu na hawan sa na sadaka yana da matuƙar wahala saboda yanayin ba shi da kyau.
Kunle ya ce ya fuskanci sanyi da iska mai tsananin gaske.Duk da wahalar tafiyar, mahayin ya yi farin ciki da ya kai shi wani muhimmin wuri kamar Millau Viaduct, wani gini mai tsayin mita 336.4 (1,104ft).
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com