28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Kashe kala: Shettima na shan zolaya a Twitter akan wankan da ya dauka zuwa taron NBA

LabaraiKashe kala: Shettima na shan zolaya a Twitter akan wankan da ya dauka zuwa taron NBA

Shettima na shan zolaya a Twitter bayan ya dauki wani wanka yayin da yaje taron Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya, NBA a ranar 22 ga watan Augustan 2022 a Jihar Legas, LIB ta ruwaito.

Shi ne dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC tare da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

A ko wanne taro, Shettima ya saba sanya manyan kaya, amma a wannan karon ya sanya wasu kananun kaya wadanda kamar sun yi masa yawa tare da takalmin zamani na Sneakers, wanda ‘yan Najeriya da dama su ka dinga ganin shigar a matsayin rashin iya sanya suttura.

Yayin da mutane ke caccakar wankan, wasu kuma sun dinga tambayar dalilin da yasa Tinubu bai je taron ba sai ya tura mataimakinsa yayin da sauran ‘yan takara su ka je da kansu.

Ga wasu daga cikin tsokacin jama’a:

Peter obi’s feminine voice tace:

“Wani ya ce ta yuwu Shettima ya sauya suttura ne a bayan mota kamar yadda fastocin bogi su ka yi. Shettiman bogi…”

Reno Omokri yace:

“Wannan shi ne mataimakin Tinubu wanda aka tsayar takara a taron NBA na yau. Kalli kafarsa. Wanne mai hankali ne zai sa kwat da madaurin wuya kuma ya sanya irin wannan takalmi yaje taro. Idan Shettima bai san yadda zai sanya sutturar da ta dace ba, ya zai yi ya kawo tallafi ga matsalolin Najeriya?”

Ademuyiwa yace:

“Mai Legas bai je taron NBA ba a Legas. Amma Peter Obi ya je, Atiku ma ya je. Mutuminka sai ya turo Shettima.”

Hotuna: Yadda ‘ya’yan marigayi Yar’adua su ka dauki wankan kece raini a liyafar auren dan’uwansu

Idan ba a manta ba, tun a makon da ya gabata aka daura auren Shehu Umaru Musa Yar’adua, wanda da ne ga tsohon shugaban kasar Najeriya, Umaru Musa Yar’adua da kuma Yacine Sheriff.

Bikin nasu ya yi matukar daukar hankali kasancewar su biyu ‘ya’yan manyan mutane ne kuma hamshakan masu kudi da masu mulki har da uwargidan shugaba Buhari, Aisha Buhari sun halarci daurin auren.

Gwamnoni, ministoci, sanatoci, manyan ‘yan kasuwa da sauran manyan mutane sun isa daurin auren a jiragen saman su fiye da goma wanda hakan ya karkatar da hankalin ‘yan Najeriya.

A wannan makon ma ba a tsaya daga bukukuwan ba, don shagulgula iri-iri kamar bridal shower, wushe-wushe da sauransu da aka dinga yi ana barin nairori.

Yayyin ango, kanni da ‘ya’yan ‘yan uwansa babu shakka sun dauki hankalin jama’a musamman idan aka kalli irin kayan alfarmar da suka sanya zuwa liyafar auren.

Sun sanya tsadaddun sarkoki da ‘yan kunnaye tare da samun masu kwalliyar da ake ji dasu don su fitar dasu kunya kuma tabbas kwalliya ta biya kudin sabulu.

Ga wasu daga hotunan kamar yadda shafukan theweddingstreet_ng da arewafamilyweddings na instagram suka nuna ‘yan uwan nasa wadanda cikinsu akwai matar tsohon gwamnan Jihar Kebbi, Dakin Gari, tsohon gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shema da sauransu.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe