27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Bidiyon da nayi ina yabon Buhari bai amfane ni da komai ba, na dawo daga rakiyarsa, Malam Nata’ala

LabaraiKannywoodBidiyon da nayi ina yabon Buhari bai amfane ni da komai ba, na dawo daga rakiyarsa, Malam Nata’ala

Jarumin kannywood, Mato Yakubu, wanda aka fi sani da Malam Nata’ala a shirin Dadi Kowa ya bayyana cewa tsohon bidiyonsa ne ake yadawa wanda aka ganshi yana yabon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A wata hira da Aminiya ta yi da shi, ya ce tun shekarar 2015 ne yayi bidiyon a lokacin mulkinsa yana farko, ba a tashi yadawa ba sai yanzu.

Malam Nata’ala ya ce a lokacin yana matukar kaunar Buhari da kuma jam’iyyar APC ne, amma banda yanzu. Kuma hakan bai amfane shi da komai ba.

Ya bayyana cewa akwai wadanda su ka dauki bidiyon su na ta yadawa yanzu da niyyar kamfen don su mori guminsa a yanzu da zabe ya matso.

Malam Nata’ala ya yi Allah ya isa ga duk wanda ya ke yada bidiyon

Ya kara da cewa:

“Zan yi wani sabon bidiyo wanda nake nisanta kaina daga wancan bidiyon da ake yadawa. Kuma Allah ya isa ga duk wanda ya ci gaba da yada shi.”

Ya ce ya janye goyon bayansa ga Buhari ne sakamakon ganin yadda talakawa ke fama da wahalhalun rayuwa da kuma tabarbarewar tsaron da ake ciki.

Sannan gwamnati ta zura ido tana kallon talaka yana fama bayan tarin gudunmawar da talakan ya bayar don ganin gwamnatin ta kafu.

Na cire tsammani daga gwamnatin Buhari – Kakakin kungiyar dattawan Arewa

Mai magana da yawun kungiyar dattawan Arewa, Emmanuel Waye, yace ya dawo rakiyar gwamnatin Buhari, bisa la’akari da yadda yake tafiyar da mulki.

Ya fadi hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin din Channels a ranar Laraba 30 ga watan Disambar shekarar 2020. Inda yake bayyana yadda rashin tsaro kullum yake kara yawaita a kasar nan.

“Ta ya za a yi a ce mutum ya kwantar da hankali a wannan halin da kasa take ciki? A baya na yarda dashi dari bisa dari, saboda ya fatattaki ‘yan kasar waje da suka zo su kashe mu,” a cewarsa.

“Lokacin da yake neman kujerar shugabancin kasa, duk mun yarda dashi. Na lura da yadda yake samun nasarar fatattakar makiyan kasar nan a 1983. Amma yanzu a garinsu kadai, an yi garkuwa da fiye da mutane 300,” ya kara da cewa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe