Shahararriyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta sha caccaka a shafinta na Twitter bayan ta saki wasu hotuna da su ka bayyana jikinta.
Hotunan sun tayar da kura inda masu zaginta su ka dinga zaginta yayin da wasu su ke mata fatan shiriya.
Ba sabon abu bane ganin jarumar da irin wannan shigar kasancewar ta dade tana janyowa kanta zagi don kusan duk shekara sai an yi caa akanta.
A wannan karon, ta saki wasu hotuna ne a Indiya inda take sanye da wata dog year da wata hula, sai dai gabadaya ilahirin kirjinta duk a waje yake.
A dayan hoton kuma wanda ta harde kafarta, zira’in kafarta duk ya bayyana yayin da alamu ke nuna ko damuwa ba ta yi ba.
Ba wannan bane karonta na farko ba da yin irin hotunan nan
Ba wannan bane karonta na farko da fara irin shigar nan ba, a shekarar da ta gabata ma ta saki wani hoto wanda har ta janyo wata ta yi suka ga fiyayyen halitta a bangaren tsokacinta.
Nan da nan mutane, malamai har da abokan sana’arta na Kannywood su ka fito fili inda su ka dinga caccakarta wasu har da zagi.
Daga bisani ta saki wani bidiyo tana kuka yayin da take ba kowa hakuri tace ita musulma ce ta kwarai kuma ba za ta taba son wani ya soki ma’aikin Allah ba.
Akwai wanda har kotu ya maka ta, wanda har maganar ta yi karfi, daga bisani dai aka warware lamarin dakyar.
A shekarun baya ta yi bikin zagayowar ranar haihuwarta sanye da kaya masu nuna tsiraici inda nan ma ta sha caccaka.
Akwai lokacin da ya kai ga har dakatar da ita daga fim aka yi a masana’antar Kannywood. Ta kuma dinga bayyana a shirye-shiryen fina-finan kudu wato Nollywood.
Yanzu haka ta tare a kasar Indiya inda ta ke taka rawa a fina-finansu wanda ciki akwai wani mai suna Khuda Hafeez. Wallafa hotunanta kadai da jaruman Indiya ya janyo mata caccaka ta ko ina.
Tsokacin mutane
Ga wasu daga cikin tsokacin mutane karkashin sabbin hotunan nata:
Mansoor Adam yace mata:
“Allah ya tsinewa masu yada fasadi. Gaskiya daya ce, ki yarda ko kar ki yarda, rigar da ki ka sanya shirmece, babu wayewa babu addini. Tabbas duk wanda yayi tsinuwa akan wannan za ta iya shafarki….
Abdurrahman bin Bala bin Abubakar yace:
“Hikimar musulunci kenan da yasa aka ce mata su zauna a gidajensu. Wallahi duk wanda kaga yana nuna ta yi kyau ba zai so ‘yar uwarsa ta zama Haka ba. Allah ya shirye ki da mu baki daya.”
Fjbeee yace:
“Anya Rahama kina tuna mutuwa kuwa?”
Sabbin hotuna da bidiyon jaruma Rahama Sadau a lokacin da take holewa ita da ‘yan uwan ta a kasar Cyprus
Rahama ta walla sabbin hotuna da bidiyo a shafinta na instagram
Jarumar ta wallafa hotunan ne a shafin ta na instagram, wanda suka ja hankalin masu kallo da sharhi kan hotunan da ta fito a ciki wadansu irin salo.
Bugu da kari, jaruma Rahamar tana nunawa yan uwan nata Soyayya, ta yadda take yin duk wani abu da zata iya yi, domin sanya musu farin ciki a koda yaushe.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com