23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Yadda wani mahaifi ya ɗirkawa ƴar sa ciki, ya tilasta mata shiga karuwanci

LabaraiYadda wani mahaifi ya ɗirkawa ƴar sa ciki, ya tilasta mata shiga karuwanci

Ƴan sanda a jihar Osun sun cafke mahaifin wata yarinya mai suna Amoda Bola, mai shekara 49, bisa zargin yiwa ɗiyar sa ciki wacce ke da shekara 14 a duniya.

Wanda ake zargin, mazaunin layin Idi Oro, Ode Remo, an cafke shi ne bayan yarinyar ta shigar da ƙorafi a ofishin ƴan sanda na Ode Remo.

Yarinyar tayi ƙorafin cewa mahaifin nata wanda suke rayuwa tare na wani lokaci ya dinga saduwa da ita. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.

Mahaifin nata yana tilasta mata kwanciya da wasu mazan

Ta kuma ƙara bayyana cewa mahaifin nata yana gayyatar wasu mazan zuwa gidan domin saduwa da ita wanda bayan sun gama saduwa da ita zasu biya shi kuɗi.

Bayan karɓar rahoton ƙorafin yarinyar, DPO na Ode Remo, CSP Olayemi Fasogbon, ya tura jami’an sa zuwa gidan inda aka cafke wanda ake zargin.

Yayin da ake masa tambayoyi, wanda ake zargin ya ƙaryata tuhumar da ake masa da farko amma daga baya ya amsa laifin sa bayan da yarinyar ta tunkare shi.

Amsa laifin da yayi ya sanya an cafke wasu mutum biyar waɗanda suka sadu da yarinyar a lokuta da dama a bisa gayyatar mahaifin nata.

Sauran waɗanda ake zargin sun haɗa da Ahmed Ogunkoya mai shekara 30, Muyiwa Adeoye mai shekara 48, David Sunday Solaja mai shekara 69, Emmanuel Olusanya mai shekara 50 da kuma Joshua Olaniran mai shekara 50.

Yarinyar na ɗauke da juna biyu

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin hukumar ƴan sandan jihar, SP Abimbola Oyeyemi, yace dukkanin waɗanda ake zargin sun amsa cewa sun sadu da yarinyar sannan sun biya mahaifin ta kuɗi.

Yace yarinyar wacce mahaifiyarta sun rabu da mahaifin nata shekarun da suka wuce, ya mayar da ita karuwa da ƙarfi da yaji.

Tuni aka kaita asibitin jiha na Isara Remo inda aka tabbatar tana ɗauke da juna biyu

Yarinyar ta haƙiƙance cewa cikin na mahaifinta ne domin shine wanda ya kwanta da ita a lokacin da ta samu cikin.

A cewar kakakin hukumar.

Yadda ɗan aikin gida ya ɗirkawa ɗiyar mai gida ciki, ya ƙona ta ƙurmus bayan zubar da cikin

A wani labarin na daban kuma wani dan aikin gida ya ɗirkawa ƴar mai gida ciki snnan ya ƙona gawarta ƙurmus.

Hukumar ƴan sandan jihar Bauchi ta cafƙe wani ɗan aikin gida mai shekara 27 bisa halaka ɗiyar mai gidan sa mai shekara 13 bayan ya ɗirka mata ciki.

Wanda ake zargin, Munkaila Ado, ya ɗirka wa yarinyar ciki sannan ya haɗa baki da mahaifiyar ta domin kai ta jihar Gombe a zubar da cikin.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe