27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Ƴan bindiga sun sace ƴan’uwan ɗan takarar gwamnan APC a Katsina

LabaraiƳan bindiga sun sace ƴan'uwan ɗan takarar gwamnan APC a Katsina

Ƴan bindiga sun kutsa cikin garin Dutsinma, hedikwatar ƙaramar hukumar Dutsinma ta jihar Katsina, inda suka sace mutum 6.

Mafi yawa daga cikin mutum 6 da ƴan bindigan suka ɗauke ƴan’uwa ne ga wanda ya nemi takarar gwamnan jihar a inuwar jam’iyyar APC, Umar Tata.

Yadda lamarin ya auku

Wasu majiyoyi sun shaidawa jaridar Daily Trust cewa wasu daga cikin mutanen da aka sace sun je ɗaurin aure ne a wani gida kusa da na ɗan siyasar.

Haka ma wata majiya mai tushe ta bayyana cewa infomomi sun taka rawa wurin yadda aka sace mutanen.

Matar da ƴaƴan ta ne da yawa daga cikin waɗanda aka sace ƴar’uwa ce ga Umar Tata, sannan ƴan bindigan kai tsaye suka kutsa gidan suka ɗauke matan, abin akwai alamar tambaya a ciki. A cewar majiyar

Ƴan bindiga sun addabi garin Dutsinma da hare-hare

Wani mazaunin garin Dutsinma wanda ya nemi a sakaya sunan shi, yace tun da farko ƴan bindigan sun sace mutum 9 a kwatas ɗin Unguwar Kudu, amma an sako mutum uku daga baya.

Da farko sun ƙyale wata tsohuwa wacce ba zata iya tafiya ba da wani yaro wanda yake sharɓar kuka. Bayan sun cigaba da tafiya kuma suka bar wata mata wacce ta gaji matuƙa.

A cikin ƴan kwanakin nan akwai lokacin da ƴan bindiga suka dinga shigowa Dutsinma kwana huɗu a jere suna sace mutane. Lamarin sai ƙara ta’azzara yake sannan mun damu sosai. A cewar majiyar

Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, kakakin hukumar ƴan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, bai tabbatar da aukuwar lamarin ba inda yace ba a sanar da shi dangane da lamarin ba, amma yayi alƙawarin zai tuntuɓi wakilin jaridar da zarar ya samu bayani.

An kama wani mutum dan kasar Nijar yana baiwa  ‘yan bindigar Katsina hayar makamai – Tsohon kakakin rundunar soji

A wani labarin na daban kuma wani mutum mai bada hayar makamai ga ƴan bindiga a jihar Katsina ya shiga hannun hukuma.

Tsohon kakakin rundunar sojin Najeriya, Gen. Sani Usman (rtd.), ya yi karin haske dangane da irin rawar da baki yan kasar Nijar ke takawa wajen tabarbarewar tsaro da ke addabar kasar Najeriya .

Da yake magana da tashar  AIT News Usman ya bada labarin wani dan Najeriya da ya zauna a jihar Katsina domin taimakawa ‘yan fashin daji. 

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe