27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Za a kammala aikin titin Kano zuwa Katsina kafin karshen shekarar 2022 –Cewar Minista

LabaraiZa a kammala aikin titin Kano zuwa Katsina kafin karshen shekarar 2022 –Cewar Minista
IMG 20220820 WA0021 1

Gwamnatin tarayya ta ce za ta kaddamar da aikin sake gina hanyar Kano zuwa Katsina kashi na daya kafin karshen wannan shekara.

Karamin Ministan ayyuka da gidaje Umar El-Yakub shi ne ya bayyana haka a ranar Asabar lokacin da ya kai ziyara inda ake gudanar da aikin a, ranar Asabar a Kano.

Ya ce kwangilar da aka bayar tun a shekarar 2013, yana daga cikin nasarorin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samu.
Mista El-Yakub ya ce hanyar tana daga cikin hanyoyi da aka bada gwangilar su,wanda ya kasance wani shiri na gwamnati don duba muhimman hanyoyi da kuma biyan ‘yan kwangilar kudadensu a kan lokaci.
“Gwamnatin Buhari tana aiki tukuru domin ganin ta kammala dukkan wadannan hanyoyin a ciki shekarar 2023,” inji shi.
Mista El-Yakub ya bukaci ’yan kwangila da su yi kokarin kammala aikin gadar Yakasai -Badume nan da bayan damina.

Zan gyara fannin Ilimi a cikin watanni 6 kacal idan aka zabe ni

Farfesa Chris Imumolen, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Accord Party APC, ya sha alwashin gyara fannin ilimin Najeriya cikin watanni shida idan aka zabe shi a zaben shekarar 2023.

Dan takarar ya kaddamar da rabon jari
Imumolen din , wanda shi ne dan takara mafi karancin shekaru a takarar shugabancin Najeriya a halin yanzu, ya yi wannan alkawarin ne yayin wani gagarumin taron tattaunawa da kungiyar PCI ta shirya a Legas.

A zaman, ya kuma kaddamar da wasu tsare-tsare na karfafawa manoma da sauran masu sana’o’i da suka hada da shirin kasuwanci na “I Will Prosper” wato “zan kudance”, domin samar ‘yan Najeriya da za su amfana daga hanyar sadarwa ta zamani, wadda zasu tara kudi ta hanyar kasuwanci.
A wannan rana, ya raba kuɗaɗen jari da yawa ga mutane daban-daban.

Fannin Ilimi shine ginshikin ko wanne dan kasa
A cewar Imumolen, jarin dan Adam na kowace kasa ya kasance ilimi shine mafi mahimmanci, dalilin da ya sa ya yi alkawarin ba shi kulawa a matsayinsa na shugaban kasa, yana mai jaddada cewa za a ware kashi 20 cikin 100 na kasafin kudin ga fannin ilimi domin tabbatar da cewa abubuwa sun yi kyau sosai.

“A matsayina na shugaban Tarayyar Najeriya, zan tabbatar da cewa za a biya malamai albashi kamar yadda ya kamata; cewa yanayin ilimi zai kasance mai kyau ga dukkan ɗalibai, kuma za su sami daidaiton al’adu tare da ɗaliban ƙasashen waje kamar yadda turawa da masu koyo daga sassa daban-daban za su ga fannin ilimin Najeriya ya burge su sosai”,

Imumolen ya yi alkawari.
ajin aikin ASUU shi ne mafita don ceto ilimin Najeriya daga rugujewa gaba ɗaya – Tsohon Shugaban Ƙungiyar
Farfesa Abiodun Ogunyemi, tsohon shugaban ƙungiyar malaman jami’o’i, ASUU, ya zargi masu riƙe da madafun iko da lalata fannin ilimi a Najeriya bisa tsari, Daily Trust ta ruwaito.

Da yake magana a safiyar Talata da gidan Talabijin na Channels, ya ce yajin aikin ASUU mafita ce ta ceto ilimin ƙasar nan daga rugujewa gaba ɗaya.

A ranar Litinin ne kungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU ta tsawaita yajin aikin na tsawon makonni 12.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe