29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

SSANU, NASU sun dakatar da yajin aikin da suka shafe watanni suna yi

LabaraiSSANU, NASU sun dakatar da yajin aikin da suka shafe watanni suna yi
ASUU

Kwamitin hadin gwiwa na jami’o’in Najeriya (JAC) da kungiyar masu zaman kansu ta kasa (NASU) da kuma manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya (SSANU) sun bayyana a ranar Laraba za su dakatar da yajin aikin da suke yi.

Sun yadda za su koma bakin aiki

Yayin da kungiyoyin jami’o’in biyu suka yadda za su koma bakin aiki, kungiyar malaman jami’o’in (ASUU) ta dage kan ci gaba da tsawaita yajin aikin da ta shafe watanni tana yi, inda ta bayyana cewa ba ta gamsu da tayin da gwamnati ta yi mata ba.

Kakakin hukumar ta JAC, Peters Adeyemi, shin ne ya sanar da matakin da NASU da SSANU suka dauka a wata sanarwa da suka bayyanawa manema labarai ranar Asabar a garin Abuja.

Sun shafe watanni suna yajin aiki

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta rawaito cewa kungiyoyin sun fara yajin aiki ne tun ranar 27 ga watan Maris domin neman a biya su wasu bukatun su.
Mista Adeyemi ya ce an dauki matakin dakatar da yajin aikin ne biyo bayan tattaunawa tsakanin kungiyoyin da tawagar gwamnatin tarayya karkashin jagorancin ministan ilimi, Adamu Adamu.

A cewarsa, dakatar da yajin aikin na tsawon watanni biyu ne domin baiwa gwamnati damar cika yarjejeniyar da aka cimma.
Daga cikin yarjejeniyar shi ne matakin da gwamnati ta dauka na ware Naira biliyan 50 domin biyan kudaden da suka samu na ilimi da alawus alawus, matakin da ya dace kan tsarin biyan albashi na jami’ar Peculiar Personnel Payroll System (U3PS).

” A cikin takardar da aka fitar kwamitin jami’o’i ta bukaci gwamnati ta biya tallafin kudaden jami’o’in da Alawus na ma’aikata.

Akan rashin tallafin da hukumomin tarayya ke samu, Ministan ya umurci hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) da ta tabbatar da cewa dukkan makarantun sun cimma abinda ake so

Ministan ilimi ya kuma ba da tabbacin cewa ba za a ci zarafin duk wani dan kungiyar da ya shiga yajin aikin ba,” in ji shi.
“Don haka, muna sanar da ku wata an koma bakin aiki na watanni biyu a matsayin gargadi ga gwamnati don cimma yarjejeniyar da aka cimma.

Addu’armu ce ta karbu, ganin irin tabbacin da Ministan Ilimi ya bada da kuma jajircewarmu na ganin an kawo karshen wannan matsala da ke faruwa.

Saboda haka, an umurci mambobin NASU da SSANU da su koma bakin aiki a ranar Laraba 24 ga watan Agusta,” inji shi.

ASUU ta mayar da martani ga Barazanar Gwamnatin tarayya:”Ba mu mutuba ba kuma baza mu mutu ba”

Yaba, Legas – Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta bayyana cewa da alama gwamnatin tarayya ta rude kan yadda tsarin jami’o’in yake,kuma kungiyar ba ta damu da matakin da gwamnati ta dauka na ‘ba aiki, ba albashi.

Ba za a biya albashi ba

Kungiyar ta bayyana hakan ne a jiya Alhamis, 18 ga watan Agusta, yayin da take mayar da martani ga furucin ministan ilimi, Adamu Adamu, inda ya ce ba za a biya malamai albashin watanni shida da suka shafe suna yajin aiki, domin hakan ya zama izini nan gaba.
Kungiyar wadda ta yi magana ta bakin shugabanta reshen jihar Legas, Adelaja Odukoya, ta ce ikirarin da kungiyar ta yi yi na cewa Transparency and Accountability Solution (UTAS) da kungiyar ta kirkiro don maye gurbin tsarin hada-hadar ma’aikata da tsarin biyan albashi, IPPIS, ba su gama tantancewa ba.

Majalisar zartarwa ta yi bayani

Odukoya, memba a majalisar zartarwa ta kasa (NEC) na ASUU, ya ce:

“Idan har wata shida ba a biya mu ba kuma ba mu mutu ba,to kuwa ba za mu mutu ba.
“Amma dole ne su sani cewa za su biya mu albashin mu. Aikin malami ya ƙunshi koyarwa, bincike da ci gaban al’umma idan bamu shiga aji ba zamu cigaba,da yin sauran abubuwan.”

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe