27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

An cafke sojoji 2 bisa halaka wani babban malami a jihar Yobe

LabaraiAn cafke sojoji 2 bisa halaka wani babban malami a jihar Yobe

An harbe har lahira wani babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Goni Aisami Gashua, akan hanyar shi daga Kano zuwa garin su na Gashua a jihar Yobe.

Ƴan sanda da shaidun gani da ido sun tabbatar da kisan malamin.

Ana zargin wasu sojoji guda biyu da halaka Malamin addinin a ranar Asabar. Jaridar Leadership ta rahoto.

Yadda aka halaka malamin

Wata majiya mai tushe ya shaidawa jaridar Leadership ta wayar tarho cewa an harbe Sheikh Goni Aisami Gashua ne har lahira a cikin motar sa.

A cewar majiyar, lamarin ya auku ne a Jaji-Maji, kilomita kaɗan daga garin Gashu da misalin ƙarfe 10 na safiyar ranar Asabar.


Ɗaya daga cikin abokansa na kusa, Hon. M. K. Gogaram ya shaidawa jaridar cewa sojojin biyu da ake zargi sun harbi malamin ne kafin nan suka ciro gawar sa daga cikin motar sannan suka yasar da ita a bakin titi.

Tuni dai aka birne malamin addinin, Sheikh Aisami, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Ƴan sanda sun tabbatar da cafke waɗanda ake zargin

A halin da ake ciki, kakakin hukumar ƴan sandan jihar Yobe, ASP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da cafke mutum biyun da ake zargi.

Yace an cafke waɗanda ake zargin ne bisa alaƙa da kisan malamin addinin Musuluncin.

Kaduna: Ƴan sanda sun cafke gawurtaccen ɗan bindiga, sun ƙwato makamai

A wani labarin na daban kuma ƴan sanda sun cafke wani ƙasurgumin ɗan bindiga, sun ƙwato makamai a jihar Kaduna. Gawurtaccen ɗan bindigan ya shiga hannu ne a wani bata kashi da jami’an hukumar suka yi da ƴan bindiga a maɓoyar su cikin dajin Galadimawa.

Jami’an ƴan sanda a jihar Kaduna sun cafke wani ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Yusuf Monore, sannan sun ƙwace bindigu biyu ƙirar AK 47/ 49 da harsasai guda biyar a hannun sa.

Kakakin hukumar ƴan sandan jihar, DSP Muhammad Jalige, a ranar Asabar yace jami’an hukumar a ranar 18 ga watan Agusta, 2022 da misalin ƙarfe 11 da minti 50 na safe, a yayin atisayen dawo da zaman lafiya a yankin Galadimawa, sun tarwatsa wata maɓoyar masu garkuwa da mutane a dajin Galadimawa

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe