27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Na sami kulawa ta musamman a gurin yan Boko Haram bayan na shida musu ni fasto ne 

LabaraiNa sami kulawa ta musamman a gurin yan Boko Haram bayan na shida musu ni fasto ne 

Wani dan aikin agaji na kungiyar kiristoci, mai suna Oyekele ya bayyana yadda ya sami kulawa ta musamman daga yan ta’addan Boko Haram. 

Yadda ‘yan ta’addan Boko Haram suka kama fasto Oyekele

A ranar 10 ga Afrilu, 2019, Oyekele ya tashi daga Maiduguri, bisa umarnin hedkwatar cocinsa na ya je ya kai kayan agaji ga sansanin ‘yan gudun hijira na Chibok. 

kulawa ta musamman
Na sami kulawa ta musamman a gurin yan Boko Haram bayan na shida musu ni fasto ne 

Wasu ‘yan kilomita kadan daga karamar hukumar Bama, sai ‘yan ta’addan Boko Haram  suka kai musu hari a kan hanya. 

Abu na farko da suka fara ji shi ne harbin bindiga. Inda suka  harbi tayoyinsu tare da kawo motocinsu da aka yi amfani da su wajen kwashe  kayan yakin da suka dauko.

Yan ta’addan sun baiwa direban motar abinci guduwa

Fasto Oyekele din,  a hirarsa da jaridar The Cable ya bayyana cewa direban motar da take dauke da kayan hatsi ya tsere ne bisa ga umarnin  ‘yan ta’addan. 

Bayan haka, daga nan aka iza keyar Mr. Oyekele,  da sauran jami’an rabon kaya, inda sai da suka yi tafiyar sa’o’i hudu zuwa sansanin ‘yan ta’addan, yayin da aka ce daya direban ya tuka motar abincin. 

Yayin da suke shiga sansanin ‘yan Boko Haram din, sai suka hadu da wasu mutanen kauyukan da yan Boko Haram suka kama. Suna ganinsu sai suka fara cewa Allahu Akbar, suna murna da kamasu.

Fasto ya boye shi waye

Oyekele ya ci gaba da bayyana wa jaridar The Cable cewa, ya boye sunan sa a matsayin Fasto ga ‘yan ta’addan Boko Haram din saboda tsoro, lokacin da aka tambaye shi.

 Ya ji yadda kiristoci, musamman ma shugabannin su,  suka fuskanci mummunan  kisa a hannun ‘yan ta’adda. Don haka ya bayyana musu cewa shi manoma ne. 

Sai dai kuma daga baya ya bayyana wa ‘yan ta’addan hakikanin waye shi, inda ya bayyana musu cewa shi Fasto ne. 

Yadda suka fara bani kulawa ta musamman

‘Yan ta’addan sun tambaye shi dalilin da ya sa ya yi musu karya, sai ya amsa da cewa ya ji abin da suke yi a lokacin da suka kama fastoci, don haka ya yanke shawarar boye hakikanin sa.

Mr. Oyekele ya bayyana cewa,  tun daga wannan rana ake yi masa wani nau’in kulawa  na daban daga ‘yan ta’adda. 

Sai suka fara ganinsa da wata fuska , inda suka fara kiransa da Baba fasto.  Bayan  an kammala tattaunawa da iyalan  sa,  an sake shi da misalin karfe daya na safiyar ranar 10 ga watan Nuwamba, 2019.

An kama wadansu mata 7 da suke kaiwa ‘yan Boko Haram kayayyakin amfani 

Sojojin Bataliya ta 195 na atisayen Hadin Kai sun kama wasu mata 7 da ke kai kayan aikace-aikace na yan  Boko Haram a wajen garin Maiduguri,  babban birnin jihar Borno.

Wadanda ake zargin sun hada da; Hadiza Ali, Kelo Abba, Mariam Aji, Kamsilum Ali, Ngubdo Modu da Abiso Lawan, da sauran su.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe