27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Kaduna: Ƴan sanda sun cafke gawurtaccen ɗan bindiga, sun ƙwato makamai

LabaraiKaduna: Ƴan sanda sun cafke gawurtaccen ɗan bindiga, sun ƙwato makamai

Jami’an ƴan sanda a jihar Kaduna sun cafke wani ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Yusuf Monore, sannan sun ƙwace bindigu biyu ƙirar AK 47/ 49 da harsasai guda biyar a hannun sa.

Yadda aka cafke ɗan bindigan

Kakakin hukumar ƴan sandan jihar, DSP Muhammad Jalige, a ranar Asabar yace jami’an hukumar a ranar 18 ga watan Agusta, 2022 da misalin ƙarfe 11 da minti 50 na safe, a yayin atisayen dawo da zaman lafiya a yankin Galadimawa, sun tarwatsa wata maɓoyar masu garkuwa da mutane a dajin Galadimawa. Jaridar Vanguard ta rahoto.

A cewar sa:

Bata kashin da akayi ya sanya jami’an sun fuskanci turjiya daga wajen ƴan bindigan waɗanda daga ƙarshe suka ranta ana kare cikin daji bayan sun samu raunika.

Sai dai, zaƙaƙuran jami’an sun samu nasarar cafke ɗaya daga cikin ƴan bindigan, mai suna Yusuf Monore, mai shekara 20 tare da bindigu 2 ƙirar AK 47/49, da harsasai guda biyar. Sauran abubuwan da aka ƙwato sun haɗa da wayoyi ƙirar Techno guda uku da fitila guda ɗaya.

Yanzu haka wanda ake zargin yana shan bincike ƙwaƙwaf yayin da jami’ai ke cigaba da neman abokan aikata ta’addancin sa.

Hukumar zata cigaba aiki tuƙuru wurin samar da tsaro a jihar

Haka kuma kwamishinan ƴan sandan jihar CP Yekini Ayoku psc (+) mni, ya yabawa jarumtar da jami’an suka nuna sannan kuma ya tabbatar da cewa jami’an hukumar da sauran jami’an tsaro za su cigaba da aiki tare domin kawo ƙarshen ƴan ta’adda a jihar.

Kwamishinan ƴan sandan ya kuma jawo hankalin mutanen jihar da su dinga kawo rahoton duk wani abu da basu yarda d shi ba ga jami’an tsaro.

Sojoji sun fatattaki ‘yan bindiga yayin da suke yin kaura zuwa wasu guraren a Kaduna

A wani labarin na daban kuma sojoji sun fatattaki ƴan bindiga a jihar Kaduna.

Sojojin Najeriya sun sake samun wasu nasarori a ci gaba da yaki da tarzoma,  ‘yan bindiga da kuma ta’addanci a kasar.

 Idan dai za’a  tunawa, a makonnin da suka gabata an yi ta samun rahotannin hare-hare ta sama da sojoji suka kai, inda suka fatattaki ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda daga maboyar su,  a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe