27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Ɗan kasuwa yasa anyi masa dandaƙa, ya bayar da dalilai

LabaraiƊan kasuwa yasa anyi masa dandaƙa, ya bayar da dalilai

Wata ɗan kasuwa mai suna Aita Joel yayi wani abin ban mamaki inda ya zaɓi da ayi masa dandaƙa bayan ya haifi yara guda biyar a duniya.

Mutumin ya garzaya zuwa shafin Twitter domin nuna yadda akayi masa dandaƙar, sannan ya bayyana dalilan da suka ja ra’ayin shi har ya kai ga ya ɗauki wannan matakin.

Ɗan kasuwar na son samun yaran da zai iya kula da su

Ɗan kasuwar ya bayyana cewa ya zaɓi da a dandake shine domin ya hana samun ƴaƴa da yawa sannan ya mayar da hankali wurin kula da ɗaukar dawainiyar waɗanda yake da su a yanzu.

A wasu lokutan, mutum yakamata ya ƙayyade haihuwa. Ya rubuta

Ya ba mazaje shawara

Daga nan kuma ya shawarci maza da su mayar da hankalin su wurin samun adadin yaran da suka san cewa za su iya kulawa da su cikin jindaɗi.

Ga abinda ya rubuta:

Bayan haihuwar yara biyar, na yanke shawarar dakatawa hakanan sannan na mayar da hankali wurin basu ingantacciyar rayuwa.

A wasu lokutan, namiji yakamata ya ƙayyade haihuwa, sannan samar da ingantacciyar rayuwa ga yaran zata ita samuwa ne kawai ga adadin da zaka iya kula da su. Ba wuya a ciki.

Idan kana son ingantaccen ilmi ga yaran ka, dole ka biya kuɗi kasa su a makaranta mai kyau. Lallai idan makarantar firamare na ƙarbar sama 20m kan kowane yaro a zango ɗaya, dole ka samu adadin da zaka iya kula da su. Ni zan iya kula da 5. Wani daban kuma zai iya kula da 10, wani kuma ƙasa da haka.

Yadda wata mata ta yankewa saurayinta mazakuta kan yunkurin yiwa ƴar ta fƴaɗe

A wani labarin na daban kuma wata mata ta yankewa saurayinta mazakuta bisa yunƙurin yiwa ɗiyarta fyaɗe.

Wata mata mai shekara 36 a duniya, ta yanke mazakutar saurayin ta mai shekara 32 a duniya, da wuƙa bisa zargin ƙoƙarin yiwa ɗiyarta mai shekara 14 a duniya fyaɗe.

Wannan lamarin ya auku ne a yankin Lakhimpur Kheri, a jihar Uttar Pradesh ta ƙasar Indiya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe