27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

An karyata Hotunan da ake alakanta su da Peter Obi wajen nuna yadda ya rushe wani masallaci a jihar Anambra

LabaraiAn karyata Hotunan da ake alakanta su da Peter Obi wajen nuna yadda ya rushe wani masallaci a jihar Anambra
Peter Obi

Wani mai amfani da shafin Twitter, Qudus Akanbi Eleyi (@Qdpaper2) ya yi ikirarin cewa Peter Obi ya rusa wani masallaci a jihar Anambra inda ya fatattaki Hausawa, Fulani da sauran ’yan Arewa mazauna jihar tun yana gwamna. An yi amfani da tarin hotuna da ke nuna wani masallaci da aka ruguje da gidajen wasu mazauna yankin.

“’Yan Arewa ba za su taba mantawa da Peter Obi da ya rusa musu masallacin su ba a jihar Anambra, Lokacin da yake gwamna, Hausawa, Fulani da ’yan Arewa za su iya yafewa Peter Obi saboda ya fatattake su daga Anambara, amma ba bu tabbacin ko za su iya yafe masa rushe masallacin su.”

Ya kasance Dan takarar Shugaban Kasa

Peter Obi shine dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LB) a zaben shugaban kasar Najeriya a 2023. Tun bayan fitowar sa a matsayin dan takarar jam’iyyar, tsohon gwamnan Anambra mai wa’adi biyu ya dauki hankalin jama’a sosai a shafukan sada zumunta, musamman a shafin Twitter, wanda ya jawo goyon baya da suka daga masu amfani da su daban-daban.

Anambara jiha ce da ke kudu maso gabashin Najeriya, yanki ne da ke da yawan al’ummar kabilar Igbo wadanda galibinsu Kiristoci ne.Sai Kabilar Fulani da Hausawa wanda galibinsu Musulmai ne.
Wani bincike da shafin Googlen ya yi a baya-bayan nan an gano cewa hoton farko, na Peter Obi da kuma masallacin da ake zargin an ruguje, an gano ainihin hoton wani masallaci ne .

Masallacin ya kasance a Zirin Gaza ne

Rahoton ya bayyana cewa masallacin ya kasance masallaci ne na Omar Ibn Abdul Aziz da ke Beit Hanoun, arewacin zirin Gaza, wanda aka lalata a lokacin rikicin Isra’ila da Falasdinu da ya barke a ranar 4 ga watan Janairun 2009.
Wannan Hoton kamar yadda ake dangantashi da jihar Anambra ba gaskiya ba ne kamar yadda ake zargin.

Afghanistan: An kai mummunan harin bam a wani masallaci, masallata da dama sun halaka

Mutane da dama sun rasa ran su bayan fashewar wani abu a wani masallaci a birnin Kabul, babban birnin Afghanistan.

A cewar BBC, fashewar ta auku ne a masallacin a ranar Laraba lokacin sallar Yamma, inda har yanzu ba a san ko mutum nawa bane suka halaka. Jaridar The Cable ta rahoto.

Hukumomi sun tabbatar da aukuwar harin
Kakakin hukumar ƴan sanda na Kabul, Khalid Zadran, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga ƴan jarida a Afghanistan, inda ya ƙara da cewa jami’an tsaro sun garzaya wurin.

Limamin masallacin yana daga cikin waɗanda suka rasu sannan da dama an garzaya da su asibiti domin duba lafiyar su.

An garzaya da waɗanda suka jikkata asibiti
Asibitin Emergency NGO, a birnin Kabul, ya rubuta a shafin Twitter cewa an kwantar da mutum 27 waɗanda harin ya ritsa da su a asibitin, ciki har da yara guda biyar.

Mun karɓi mutum 27 a asibitin mu ya zuwa yanzu bayan fashewar wani abu a yankin PD17. Asibitin ya rubuta.

Akwai yara guda biyar daga cikin su, ciki hada mai shekara bakwai a duniya.

Harin na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan an halaka Rahimullah Haqqani, wani babban malami a Afghanistan, a harin ƙunar baƙin wake na bam a Kabul.

Ƙungiyar ta’addanci ta Islamic State (IS) ta ɗauki alhakin halaka malamin wanda aka kai wa hari saboda yana goyon bayan karatun mata.

Taliban ta umarci mata masu gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin da su din ga rufe fuskokinsu
A wani labarin na daban kuma, Taliban ta hana mata masu gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin su dinga kulle fuskokin su.

Hukumomin Taliban a ranar Alhamis sun ba da umarni a hukumance cewar dole ne ‘yan jarida mata a dukkan kafafen yada labarai na Afghanistan da su fara rufe fuskokinsu yayin da suka fito don gabatar da shiri a gidan talabijin.

Kafofin yada labarai na cikin gida na Afganistan sune suka ruwaito a ranar Alhamis cewa an kafa wannan doka ga duk gidajen talabijin dake fadin kasar,sun kara da cewa hakan doka ne ba shawara ba.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe