27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Harin Jirgin Kasan Kaduna: ‘Yan Ta’adda Sun Sake Sako Fasinjoji 4

LabaraiHarin Jirgin Kasan Kaduna: 'Yan Ta'adda Sun Sake Sako Fasinjoji 4

Halimatu Attah, tsohuwa mai shekaru 90 da aka yi garkuwa da ita a farmakin da ‘yan ta’adda suka kai wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a watan Maris ta shaki iskar ‘yanci.

An sakota tare da diyarta da wasu mutum biyu kamar yadda mawallafin jaridar Desert Herald, Tukur Mamu ya bayyana, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Harin Jirgin Kasan Kaduna: 'Yan Ta'adda Sun Sake Sako Fasinjoji 4
Harin Jirgin Kasan Kaduna: ‘Yan Ta’adda Sun Sake Sako Fasinjoji 4

“Zan iya tabbatar muku da cewa a sa’o’in farko na ranar Juma’a, maharan jirgin kasan sun sake sakin wasu mutum hudu daga cikin wadanda suka yi garkuwa da su.

“Daga cikinsu wadanda aka saki a ranar Juma’an akwai wata tsohuwa wacce tafi kowanne fasinja shekaru, Mama Halimatu Attah. Tana da shekaru 90 a duniya. Sun kara da sako diyarta mai shekaru 53 mai suna Adama Atta Aliyu.

“Mutum hudun da aka saki yanzu suka bar ofishina. Sun ce sun zo ne domin yi min godiya kan kokarin da na dinga wurin sasancin sako su da kuma yadda na dinga kokarin ganin cewa ‘yan ta’addan sun ajiye barazanar halaka su. Yadda na dinga shiga da fice wurin masu ruwa da tsaki balle gwamnatin tarayya don ganin sun fito. Akwai sauran mutum 23 a dajin kuma cikin mawuyacin hali,” ya sanarwa da manema labarai.

Sauran biyun da aka sako tare da tsohuwar sune Muhammad Sani Abdulmajid wanda aka fi sani da M. S Ustaz da kuma Alhaji Modin Modi Bodinga.

Idan na ci nasara, har da ni za a dinga 6uruntun ‘yan ta’adda, Dr Dikko Radda

Dr Umar Dikko Radda, dan takarar gwamnan Jihar Katsina karkashin jam’iyyar APC, ya bayyana irin gudunmawar da zai bayar don gyara akan matsalar tsaron da ta addabi jihar.

Yayin tattaunawa da BBC Hausa a shirinsu na Daga Bakin Mai Ita, ya bayyana wurare daban-daban da yayi aiki, kuma a cewarsa, mawuyacin halin da mutane ke ciki ne ya ba shi kwarin gwiwar takarar.

Ya bayyana cewa:

“Ni tsohon malamin makaranta ne, tsohon ma’aikacin banki ne, tsohon shugaban karamar hukuma ne na shekaru. Na yi aiki a majalisar tarayya. Na yi aiki a National Working committee na APC na farko da aka zaba a jam’iyya a 2014.

“Na yi shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Jihar Katsina. Na yi shugaban kanana da matsakaitan masana’antu na kasa na shekara 6. Ni ne shugaban kanana da matsakaitan masana’antu na farko da aka maimaitawa kujerarsa tunda aka kafa hukumar.”

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe