28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Hukumar Hisbah ta ƙona kwalaben giya na maƙudan kuɗaɗe a Jigawa

LabaraiHukumar Hisbah ta ƙona kwalaben giya na maƙudan kuɗaɗe a Jigawa

Hukumar Hisbah ta jihar Jigawa ta ƙona kwalaben giya sama da 5,550 wanda darajar kuɗin su takai N3.2m. 

Da yake magana bayan kammala aikin a ƙaramar hukumar Kazaure ta jihar, shugaban hukumar na jihar Jigawa, Ibrahim Dahiru, yace kayan mayen an kama su ne a zagayen da hukumar ke gudanarwa yanzu. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.

Ya bayyana adadin giyar da aka ƙwato

A cikin sati biyu mun ƙwace giya ta kai kwalabe 5,500 wanda kuɗin su yakai N3.2m. A cewar sa

Dahiru yace an gudanar da aikin ne bayan samun izni daga kotu wanda ya bayar da damar lalata giya.

Addinin musulunci ya hana shan giya d sauran kayan maye masu gusar da hankalin ɗan Adam, hakan yasa Hisbah ke ƙoƙarin tabbatar da kare lafiyar mutanen jihar nan.

A musulunci an haramta shan giya. Dokar jihar Jigawa ta haramta sha da cinikayyar giya.

Hukumar Hisbah zata ƙara zage damtse wurin hana shan giƴa

Dahiru yace hukumar zata cigaba wurin ƙara ƙaimi a faɗan da take da duk wani abun baɗala a jihar domin tabbatar da lafiya da jindaɗin mutanen jihar.

Shugaban ƙaramar hukumar, Muhammad Muktar, wanda yana wurin lokacin da ake ƙona kwalaben, ya yabawa Hisbah bisa nasarar da suka samu na ƙwace kayan mayen.

Hukumar KAROTA tayi babban kamu, ta cafke babbar mota maƙare da giya a jihar Kano

A wani labarin na daban kuma hukumar KAROTA ta cafke wata babbar mota maƙare da barasa a jihar Kano. Hukumar ta kuma wani jami’inta tukuici bisa ƙin karbar kuɗin goro da yayi domin ya saki motar.

Hukumar KAROTA ta jihar Kano, ta samu nasarar tare wata motar dakon ƙaya maƙare da giya wacce takai darajar maƙudan kuɗaɗe har N50m.

Kakakin hukumar, Nabilusi Abubakar, ya bayyana cewa giyar takai kiret 2000 a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 28 ga watan Yulin 2022.

Babban darektan gudanarwa na hukumar, Hon. Baffa Babba Dan Agundi, wanda ya tabbatar da kamen ya kuma ba jami’in da ya tare motar tukwuicin N1m saboda ƙin karɓar cin hancin N500,000 domin ya saki kayan.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe