23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Kotu ta daure matashin da ya gannara wa dan shekara 8 cizo a kirji

LabaraiKotu ta daure matashin da ya gannara wa dan shekara 8 cizo a kirji

Kotu ta yanke wa wani mutum mai suna Thomas Cockings watanni 15 a gidan yari bayan ya gannara wa dan shekara 8 cizo a kirji sannan ya musanta aikata hakan, LIB ta ruwaito.

Wata kotun Swansea Crown da ke Birtaniya ta samu bayani akan yadda matashin ya kai yaron kusa da karensa duk don ya tsorata shi. Ya kuma nemi idan yaron ya je gida ya ce wa mahaifiyarsa cewa da kwallo ya buge a lokacin da yake wasa.

Mai gabatar da kara, Leuan Rees ya ce yaron ya isa gida da yamma lokacin ranin shekarar 2021 inda mahaifiyarsa ta kula da alamar cizo a kafadarsa.

Yayin da yaron ya sanar da mahaifiyarsa cewa kare ne ya cije shi, ta gano wata alamar cizo a kirjinsa wacce ta yi kama da mutum ne yayi cizon.

Daga nan ne yaron yace mata yayin wasa da kwallo ne ya fadi yaji ciwon. Sai dai mahaifiyarsa bata yarda ba inda ta kira wayar gaggawa ta 101, daga nan ne aka shawarce ta da kai shi asibiti don gudun wata cuta ta same shi.

Daga nan ne ta kai yaron zuwa asibitin Morriston, bangaren gaggawa inda a lokacin ne yaron ya bayyana dan shekara 29 da ya gannara masa cizo.

Bayan sanar da jami’an tsaro ne aka tura yaron asibitin Swansea’s Singleton inda aka duba shi sosai. Anan ne aka kama Cockings yayin da ya sha tambayoyi. Ya sanar da jami’an tsaro cewa karenshi ne ya ciji kafadar yaron.

An gabatar da hoton kafada da kirjin yaron inda alamu su ka bayyana cewa tabbas cizon hakorin mutum ne.

Daga bisani Cockings ya amsa laifin cutar da yaron duk da dai da farko ya musanta.

Lauyan Cockings, John Allchurch, ya ce wanda yake karewa yana fama da cutar tabin hankali ne tun yana yaro.

Alkali Paul Thomas QS ya sanar da Cockings yadda abin da yayi ya cutar da yaron kasancewar alamar hakoransa sun bayyana a kirjin yaron kuma ya yi matukar razanar da shi. Wannan dalilin yasa ya yanke masa hukuncin daurin watanni 15 a gidan yari.

Kotu ta daure wani matashi bayan karuwa ta mutu su na tsaka da lalata

Augustine ta bayyana yadda mamaciyar ta shiga mawuyacin yanayi yayin da su ke tsaka da lalatar wacce ta yi sanadin mutuwarta.

Ana zarginsa da aikata laifin ne a ranar 22 ga watan Yunin 2022, da misalin karfe 4 na safiya a Otal din Cool Corner cikin Ondo, sai dai bai amsa laifin ba.

A cewarsa Augustine, laifin ya ci karo da sashi na 316(2) kuma hukuncinsa na karkashin sashi na 319 na dokar Criminal Code Cap 37. Volume 1, na dokokin Jihar Ondo, 2006.

Lauyan wanda ake zargi, C. O Falana ya bukaci kotu ta ba shi damar yin rantsuwa.

Alkalin kotun, O. R Yakubu ya bukaci a sakaya wanda ake zargin a magarkamar ‘yan sanda sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 14 ga watan Yulin 2022.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe