34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Ma’aikatan hukumar muhalli masu zanga-zanga sunyi barazanar kulle makabartun Abuja baki daya

LabaraiMa'aikatan hukumar muhalli masu zanga-zanga sunyi barazanar kulle makabartun Abuja baki daya

Ma’aikatan hukumar muhalli, a babban birnin tarayya Abuja, sun yi barazanar rufe daukacin  makabartar jama’a dake Abuja.

Fusatattun  ma’aikatan sun danganta daukar matakin nasu ne da gazawar mahukuntan  babban birnin tarayya ta Abuja, wajen aiwatar musu da sabon tsarin albashi. 

hukumar muhalli
Ma’aikatan hukumar muhalli masu zanga-zanga sunyi barazanar kulle makabartun Abuja baki daya

sun sake budeta bayan matsin lamba

Ma’aikatan, wadanda tun farko suka kulle makabartar Gudu,  a babban birnin Abuja , sun sake budeta bayan matsin lamba da suka sha daga fadar shugaban kasa, inda suka bude ta a safiyar ranar Alhamis.

Matakin kulle makabartun ya biyo bayan  gazawar da Hukumar Abuja  ta yi, na kin aiwatar da sabon tsarin albashi ga ma’aikatan.  Kamar  yadda jaridar Aminiya ta ruwaito.

Muktar Bala, Shugaban Kungiyar, shugaban Hadaddiyar kungiyar hadin kan jama’a, kungiyar hidimar al’umma fasaha da nishadi,(AUPCTRE) mai suna (AEPB) , ya ce duk da cewa kungiyar ta amince da bude wasu makabartu, amma za ta sake garkame su, idan ba a biya musu bukatunsu ba.

Shugaban kungiyoyin ma’aikatan ya nuna damuwar sa ga halin da suke ciki

Bala, wanda ya nuna damuwarsa kan halin da ma’aikatan hukumar ke ciki, game da jin dadin yan kungiyar, ya ce suna fuskantar matsaloli ga  lafiyar su yayin kula da gawarwakin da aka rasa masu su.

Ya kara da cewa, 

A matsayina na shugaban daya daga cikin kungiyoyi na AEPB, ina mai tabbatar muku da cewa wannan shawara ce ta gamayyar  kungiyoyin mu baki daya, tare da goyon bayan uwar kungiya ta kasa. 

Mutane suna tunanin sarrafa shara ne kawai aikin mu. Ba su san cewa ko gawarwakin da aka rasa masu su, a  asibitoci mu ne ke kula da su ba.

“Wadannan gawarwakin da suka wuce shekaru 3 zuwa 4 suna kwance a asibiti, mu muke kula da su, ba tare da sanin me ya kashe su ba.

 

“Asibitoci na zuwa wurinmu ne a lokacin da suke son a yi Janaiza, ga irin wadannan gawawwakin. Idan akwai gawarwakin  da ba’a nema ba, ko ba’a samu masu su ba, a kan hanya ko kuma a wasu wurare, ‘yan sanda za su rubuta rahoto su kawo mana domin  binne su.

Duk waɗannan hadari,  mutane ba sa kallon cewa muna yin wani abu. Muna so mu gaya wa gwamnati cewa banda  sarrafa sharar, muna yin wasu abubuwan ma.

“A bisa shawarar da kungiyar hadin gwiwa ta AEPB ta yanke a daren jiya, mun amince da bude makabartar da karfe 9 na safiyar Alhamis saboda kiran fadar shugaban kasa. Duk da haka, idan ba a cimma yarjejeniyar mu ba, to  kawai za mu rufe makabartu, gami da dukkan  ayyukanmu,” inji shi.

Shan taba yana ƙara raguwa- Inji Hukumar lafiya ta duniya

Hukumar lafiya ta duniya, tace adadin kasashen da suke kan kadamin rage shan taba da kaso talatin 30 bisa dari, tsakanin shekarar 2010 zuwa 2025, ya kara linkuwa daga kasashe 32 zuwa kasashe 60. Jaridar Punch ta rahoto.

Ƙasashen duniya da dama na rage amfani da taba

Shugaban hukumar ta WHO chief, Tedros Ghebreyesus, wanda ya sanar da hakan a ranar Litinin, a taron hukumar lafiyar na duniya, ya bayyana cewa, kasashen duniya da dama suna karuwa wajen kokarin rage amfani da tabar mai matukar hadari ga lafiya.

 kokarin saisaita tasirin cututtuka masu yaduwa kasashe da dama suna kokarin gaske, wajen rage amfani da kayayyaki masu matukar hadari ga lafiya.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe