34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Shahararren mawaƙin Amurka Wiz Khalifa ya nuna goyon bayan sa ga Palasɗinawa

LabaraiShahararren mawaƙin Amurka Wiz Khalifa ya nuna goyon bayan sa ga Palasɗinawa

Shahararren mawaƙin gambara na Amurka Wiz Khalifa, ya nuna goyon bayan sa kan mutanen ƙasar Palasɗinu bisa wahalar da suke sha a hannun sojojin ƙasar Isra’ila.

Mawaƙin yabi sahun sannannun taurarun mutanen da suka nuna goyon bayan su kan Palasɗinawa bisa azabtar da su d sojojin Isra’ila ke yi. Jaridar The Islamic Information ta rahoto.

Wiz Khalifa ya ɗaga tutar Palasɗinu

A ranar 9 ga watan Agusta, wani amfani da shafin TikTok mai suna @nooriiqaddoura, ya sanya wani bidiyo wanda ya nuna Wiz Khalifa yana ɗaga wani kallabi mai ɗauke da tutar Palasɗinu ga masoyansa a kan dandali yayin da yake wata waƙarsa a wurin wani wasansa a birnin Dallas na ƙasar Amurka.

Kafin fara waƙar mai suna “See You Again,” Wiz Khalifa ya nuna goyon bayan sa ga Palasɗinawa.

Jaruman Amurka da dama na goyon bayan Palasɗinu

Jaruman fim da dama daga Amurka sun nuna goyon bayan su ga Palasɗinawa inda suka yi Allah wadai da hare-haren da Isra’ila ke kaiwa ƙasar Palasɗinu, waɗanda suka halaka farar hula da dama sannan da tilasta wasu da yawa rayuwa cikin fargaba.

Fitattun taurari biyu ƴan’uwan juna Gigi Hadid Bella Hadid na daga cikin taurarin da suka fi nuna goyon bayan su kan ƴancin Palasɗinawa a shafukan sada zumunta. Suna yawan nuna goyon bayan su ga Palasɗinu inda nan ne aka haifi mahaifin su duk kuwa da tsanar da ake nuna musu idan sun yi.

Sauran fitattun taurari da suka haɗa da jarumi Mark Ruffalo, Susan Sarandon, Gael García Bernal, Viggo Mortensen, da sauran mutane da dama a masana’antar Hollywood, har wata takarda suka sanya wa hannu domin nuna goyon bayan su ga abokiyar aikin su Emma Watson, bayan ta saka wani hoto mai nuna goyon baya ga Palasɗinawa wanda aka rubuta “haɗin kai ma wani yunƙuri ne”

Palasɗinawa na shan wuya a hannun sojojin Isra’ila

Cikin ƴan kwanakin nan Palasɗinawa a zirin Gaza sun ƙara shiga cikin mawuyacin hali lokacin da Isra’ila ta ƙaddamar da hare-hare ta jirgin sama a faɗan kwana uku da masu rajin kare ƴancin Palasɗinawa a zirin Gaza.

Faɗan ya tsaya ne kawai lokacin da sojojin  Isra’ila da ƙungiyar masu rajin kare Palasɗinawa suka sanar da tsagaita wuta a ranar Lahadi 7 ga watan Agusta, 2022.

Ministirin lafiya ta ƙasar Palasɗinu ta samar cewa faɗan na zirin Gaza daga 5 zuwa 7 ga watan Agusta, yayi sanadiyyar rasuwar mutum 49, ciki har da ƙananan yara 17 da mata 4 sannan wasu mutum 360 sun jikkata.

Ran Yahudawa ya baci bayan fitacciyar jaruma Emma Watson ta nuna rashin jin dadinta kan cin zarafin Palasdinawa da suke yi

A wani labarin na daban kuma ran Yahudawa ya ɓaci bayan fitacciyar jaruma ta nuna rashin jindaɗin ta kan cin zarafin Palasɗinawa da suke yi.

A shafin ta na Instagram, fitacciyar jarumar kasar Amurka ta kamfanin Hollywood, Emma Watson, wadda tayi suna a cikin Fim din “Harry Potter”, ta nuna goyon bayan ta ga Palasdinawa a wani sabon sako da ta saki.

Abin da ya jawo mata gagarumin goyon baya daga wajen Palasdinawa, kuma ya Jawo mata kakkausan suka daga wajen Yahudawan kasar Isra’ila.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe