Farfesa Chris Imumolen, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Accord Party APC, ya sha alwashin gyara fannin ilimin Najeriya cikin watanni shida idan aka zabe shi a zaben shekarar 2023.
Dan takarar ya kaddamar da rabon jari
Imumolen din , wanda shi ne dan takara mafi karancin shekaru a takarar shugabancin Najeriya a halin yanzu, ya yi wannan alkawarin ne yayin wani gagarumin taron tattaunawa da kungiyar PCI ta shirya a Legas.
A zaman, ya kuma kaddamar da wasu tsare-tsare na karfafawa manoma da sauran masu sana’o’i da suka hada da shirin kasuwanci na “I Will Prosper” wato “zan kudance”, domin samar ‘yan Najeriya da za su amfana daga hanyar sadarwa ta zamani, wadda zasu tara kudi ta hanyar kasuwanci.
A wannan rana, ya raba kuɗaɗen jari da yawa ga mutane daban-daban.
Fannin Ilimi shine ginshikin ko wanne dan kasa
A cewar Imumolen, jarin dan Adam na kowace kasa ya kasance ilimi shine mafi mahimmanci, dalilin da ya sa ya yi alkawarin ba shi kulawa a matsayinsa na shugaban kasa, yana mai jaddada cewa za a ware kashi 20 cikin 100 na kasafin kudin ga fannin ilimi domin tabbatar da cewa abubuwa sun yi kyau sosai.
“A matsayina na shugaban Tarayyar Najeriya, zan tabbatar da cewa za a biya malamai albashi kamar yadda ya kamata; cewa yanayin ilimi zai kasance mai kyau ga dukkan ɗalibai, kuma za su sami daidaiton al’adu tare da ɗaliban ƙasashen waje kamar yadda turawa da masu koyo daga sassa daban-daban za su ga fannin ilimin Najeriya ya burge su sosai”,
Imumolen ya yi alkawari.
ajin aikin ASUU shi ne mafita don ceto ilimin Najeriya daga rugujewa gaba ɗaya – Tsohon Shugaban Ƙungiyar
Farfesa Abiodun Ogunyemi, tsohon shugaban ƙungiyar malaman jami’o’i, ASUU, ya zargi masu riƙe da madafun iko da lalata fannin ilimi a Najeriya bisa tsari, Daily Trust ta ruwaito.
Da yake magana a safiyar Talata da gidan Talabijin na Channels, ya ce yajin aikin ASUU mafita ce ta ceto ilimin ƙasar nan daga rugujewa gaba ɗaya.
A ranar Litinin ne kungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU ta tsawaita yajin aikin na tsawon makonni 12.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka: