23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Direbobin tanka sun tare hanyar Zaria zuwa Kano bisa rauni da ‘yan KASUPDA su ka yiwa dan uwan su

LabaraiDirebobin tanka sun tare hanyar Zaria zuwa Kano bisa rauni da 'yan KASUPDA su ka yiwa dan uwan su
Tanker Drivers in Abia 811182537.jpeg

A ranar Alhamis din da ta gabata direbobin tankar Mai suka tare hanyar Zariya zuwa Kano na tsawon sa’o’i takwas bayan da wasu ma’aikatan hukumar raya birane ta jihar Kaduna (KASUPDA) suka yi wa wani direba rauni, a sakamon sayar da sitika ga direbobi.

Direbobi sun toshe hanya

Wakilinmu da ya ziyarci wurin, ya ruwaito cewa direbobin sun tare hanyar Zabi da ke unguwar Dogarawa a karamar hukumar Sabon Gari ta Jihar Kaduna daga karfe 6:15 na safe zuwa karfe 2 na rana, inda suka toshe hanya na tsawon kusan kilomita 40.

Yan KASUPDA sun daki direba

Direban da ya samu rauni, Malam Bawa Isah, wanda ya taso daga Legas zuwa Kano, ya ce “Ma’aikatan Hukumar Raya Birane ta Jihar Kaduna, KASUPDA su kusan shida ne da suka ba direbobin tanka sitika, su ne suka haddasa tarewar hanya.

Na ajiye mota ta a gefen hanya.Kawai na ga ma’aikatan KASUPDA suna cire min batir, sai suka fara dukana. Hakan ya haifar da gocewar kafada ta.
“Isowar abokan aikina ne ya cece ni daga.inda suka taru a wurin.
“Wannan shine dalilin da yasa abokan aikina suka yanke shawarar tare hanya har sai hukumomi sun sa baki tare da daukar matakan da suka dace akan ma’aikatan da suka yi kuskure.”

Jami’in hulda ya yi bayani

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na KASUPDA, Malam Nuhu Mohammed, wanda ya yi alkawarin dawowa bayan samun cikakken bayanin faruwar lamarin, bai mayar da martani ba har zuwa lokacin da aka mika rahoto.

Asiri ya tonu: An cafke wani mutumi na ƙoƙarin aika bindigu zuwa Kano daga Abuja

Mambobin ƴan sintiri a tashar motar Zuba da ke babban birnin tarayya Abuja, sun cafke wani mutum da bindigogi takwas da ya yi niyyar kai su jihar Kano.

Jaridar Daily Trust ta rahoto shugaban ƴan sintirin da ke yankin, Yahaya Madaki, yana cewa lamarin ya auku a ranar Laraba da misalin ƙarfe biyu na rana, inda wanda ake zargin yazo wata tashar mota a bakin titi kusa da wani gidan mai, wanda a da aka fi sani da Dan-Kogi, yana neman motar da zata Kano.

Daga nan sai aka haɗa shi da direban da ke lodi zuwa Kano a lokacin ya miƙa masa sakon wanda aka rufe a cikin kwali da kuma lambar wayar mutumin da zai ba saƙon idan ya isa Kano.
An caji mutumin naira dubu 10 a matsayin kuɗin dakon kayan, wanda nan take ya ciro ya bayar, daga nan ne sai direban motar ya nemi sanin abinda ke a cikin kwalin inda mutumin yaƙi yarda. Ana cikin haka kawai sai mutumin ya nemi ya ranta a na kare sai akayi caraf da shi.

A cewar Yahaya
Yahaya Madaki ya ƙara da cewa ko da aka bude kwalin an ga bindigu ƙirar AK-47 guda biyar, da ƙananan bindigu uku.

DPO ɗin Zuba, CSP Osor Moses, shine ya jagoranci tawagar ƴan sandan da suka kama wanda ake zargin.

Ƙoƙarin jin ta bakin ƴan sanda yaci tura
Ko da wakilin jaridar ya nemi jin ta bakin DPO ɗin, sai yaƙi cewa komai, sai kawai ya tura shi ya tuntuɓi ofishin hukumar na Abuja.

A na ta ɓangaren, kakakin hukumar ƴan sandan Abuja, Josephine Adeh, tayi alƙawarin yin bincike kan lamarin kafin ta ce komai, sai dai har zuwa lokacin da aka kammala haɗa wannan rahoton, ba aji daga gare ta ba.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe