24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

ASUU ta mayar da martani ga Barazanar Gwamnatin tarayya:”Ba mu mutuba ba kuma baza mu mutu ba”

IlimiASUU ta mayar da martani ga Barazanar Gwamnatin tarayya:"Ba mu mutuba ba kuma baza mu mutu ba"
a7519b4f4fb5b7d5
“Ba mu mutuba ba kuma baza mu mutu ba”

Yaba, Legas – Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta bayyana cewa da alama gwamnatin tarayya ta rude kan yadda tsarin jami’o’in yake,kuma kungiyar ba ta damu da matakin da gwamnati ta dauka na ‘ba aiki, ba albashi.

Ba za a biya albashi ba

Kungiyar ta bayyana hakan ne a jiya Alhamis, 18 ga watan Agusta, yayin da take mayar da martani ga furucin ministan ilimi, Adamu Adamu, inda ya ce ba za a biya malamai albashin watanni shida da suka shafe suna yajin aiki, domin hakan ya zama izini nan gaba.
Kungiyar wadda ta yi magana ta bakin shugabanta reshen jihar Legas, Adelaja Odukoya, ta ce ikirarin da kungiyar ta yi na cewa Transparency and Accountability Solution (UTAS) da kungiyar ta kirkiro don maye gurbin tsarin hada-hadar ma’aikata da tsarin biyan albashi, IPPIS, ba su gama tantancewa ba.

Majalisar zartarwa ta yi bayani

Odukoya, memba a majalisar zartarwa ta kasa (NEC) na ASUU, ya ce:

Idan har wata shida ba a biya mu ba kuma ba mu mutu ba,to kuwa ba za mu mutu ba.
“Amma dole ne su sani cewa za su biya mu albashin mu. Aikin malami ya ƙunshi koyarwa, bincike da ci gaban al’umma idan bamu shiga aji ba zamu cigaba,da yin sauran abubuwan.”

Kada ku zabi duk wani dan siyasa da ‘yayan sa suke kasar waje suna karatu – Inji ASUU ga yan Nageriya

Farfesa Emmanuel Osodeke, shugaban kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU, ya bukaci daliban Najeriya da kada su zabi ‘yan siyasar da ‘ya’yansu ke karatu a makarantun kasashen waje.

Oloyede din ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 17 ga watan Agusta, yayin da yake magana a shafin yanar gizo na Tuwita na gani gaka, wanda jaridar Premium Times ta shirya mai taken, “ASUU, da kudaden farfado da jami’oi in mafita.”

kada dalibai su zabi duk ‘yan siyasar da basa kishin alumma
Da yake ba da shawarar yadda za a kawo karshen yajin aikin na kungiyar ta ASUU, ya ce kada dalibai su zabi duk ‘yan siyasar da ba za su wakilci muradunsu ba.
Osodeke din ya kara da cewa ,

“Duk wanda kuka yi imani ba zai iya biyan bukatunku ba, wanda ‘ya’yansa ke karatu a kasashen waje, kuma auke zaune a kasashen wajen, to kada ku zabe su, ina kara maimaitawa, ba kwa bukatar ku zabe su, domin ba zaku zabi mutanen da ke son ganin bayan ku ba”.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe