Tauraruwar (Big Brother Naija ) wacce aka fi sani da Erica Nlewedim, ta samu sharhi kala kala, a yanar gizo, karon farko da tayi wata shiga mai kyawu ba tare da ta yi shafeshafen kwalliya ba.
Ba na bukatar yin kwalliya kafin na yi kyawu
Tauraruwar wacce kuma yar kasuwa ce, ta yada wani hoton ta a yanar gizo, inda ta fadi dalilan da suke nuna cewa bata bukatar yin kwalliya kafin ta yi kyawu.

Da take yada hoton a tabbataccen shafinta na Instagram, Erica din ta kula cewa gaba daya farin ciki ta zaba wanda shine ita kanta, kuma za ta ci gaba da kasancewa kyakkyawa har sai ta kai shekaru 90.
Rubutun da ta kwarzanta kanta da kanta
Ta rubuta:
” Na zabi farin ciki! Na zabi kai na! Zan rayu kyakkyawar rayuwa, kuma zan kasance kyakkyawa har sai na kai shekara 90! Babu kayan shafa”
Shahararrun jarumai da suka hada da Jackie B, Uti Nwachukwu, Mercy Atang, Toni Tones, da sauran masoyan Erica Nlewedim sun yi sharhi mai kyau dangane da hoton nata marar kwalliya.
Mayafin fuska ya na bai wa mata lafiya, kyalli da kyawun fata – Kwararrun Fata
Sirrin da ke tattare da fatar matan larabawa mara aibi: Saboda yadda ake yawan kamuwa da gurbatar yanayi, duk masanan fata a halin yanzu sun bayyana cewa dalilin da ya sa fatar matan Larabawa ta yi rashin aibi shi ne saboda rufe fuska. Hakan ba wai kawai ya na kare su daga illar rana ba har ma da gurɓacewar yau da kullum.
Hayaki da ke fitowa daga masana’antun da ke kusa, iskar gas da ake fitarwa daga motoci tare da sare bishiyoyi suna rage yawan oxygen da ke cikin iska. Iskar ta gurbata ta yadda ko batare da wata alaka da datti ba; Fuskarmu a ƙarshen wuni ana samun idan an goge da ƙyallen goge fuska.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com