31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Sojoji sun fatattaki ‘yan bindiga yayin da suke yin kaura zuwa wasu guraren a Kaduna

LabaraiSojoji sun fatattaki 'yan bindiga yayin da suke yin kaura zuwa wasu guraren a Kaduna

Sojojin Najeriya sun sake samun wasu nasarori a ci gaba da yaki da tarzoma,  ‘yan bindiga da kuma ta’addanci a kasar.

An fatattaki ‘yan bandiga a hare-haren da sojoji suka kai

 Idan dai za’a  tunawa, a makonnin da suka gabata an yi ta samun rahotannin hare-hare ta sama da sojoji suka kai, inda suka fatattaki ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda daga maboyar su,  a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan.

yan bindiga

Sai dai a cewar rahotannin baya-bayan nan, rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar kashe wasu ‘yan bindiga da ke yin hijira zuwa wani yanki da ke kusa da Ungwan Namama da kuma kan hanyar Zariya zuwa Kano a jihar Kaduna.

Kwamishinan Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Kaduna  Samuel Aruwan,    shine ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

Yadda artabun ya faru

Ya bayyana cewa, a yayin da  dakarun sojin da ke sintirin da suka saba yi, sun ci karo da ‘yan ta’addan da ke yankin,  inda suka fafata da su, abin da ya tilasta yan ta’addan suka gudu  suka yi watsi da mutane guda uku da suka kamo da kuma  wasu dabbobi.

A cewar kwamishinan, sojojin sun samu nasarar kubutar da mutanen uku da aka yi garkuwa da su, da wadansu dabbobi guda tara da suka sato daga wata jihar da take makwabtaka da su.

An kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su

 Wadanda aka yi garkuwa da su din sun hada da : Abdullahi Lawal, Sadiya Salimanu, Fatima Salimanu da kuma yarinyar Sadiya mai watanni 10, duka an kubutar da su, inda suka sake haduwa da iyalansu.

 ‘Yan bindiga sun halaka sojoji sun yi awon gaba da ‘yan ƙasar Chana a jihar Neja

‘Yan bindiga sun kai hari a wurin wani haƙar ma’adanai a jihar Neja, inda suka halaka jami’an tsaro, farar hula sannan su kayi awon gaba da ‘yan ƙasar Chana mutum uku.

An bayyana wurin da su ka kai harin

Jaridar The Punch ta rahoto cewa harin ya auku ne a ranar Laraba da misalin ƙarfe huɗu na yamma a ƙauyen Ajata, Aboki cikin garin Gurmana na ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Shugaban wata ƙungiyar matasa ta ‘Concerned Shiroro Youth of Niger State’ Sani Kokki, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Alhamis.

u cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe