27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Cikin ruwan sanyi APC zata lashe zaɓen 2023 -Gwamna Masari

LabaraiCikin ruwan sanyi APC zata lashe zaɓen 2023 -Gwamna Masari

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, yace jam’iyyar APC ba zata sha wuya ba wurin lashe babban zaɓen 2023.

Masari ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da ƴan jarida ranar Laraba jim kaɗan bayan ya ƙaddamar da wani ɗakin kwanan ɗalibai da aka sanya wa sunan sa a jami’ar Al-Hikmah a jihar Kwara. Jaridar The Cable ta rahoto.

Masari ya soki masu ganin APC ba zata kai labari ba

Masari yace waɗanda ke cewa APC ba zata kai labari ba a zaɓen “basu san abinda suke cewa ba gabaɗaya”.

Gwamnan yace matsalolin dake addabar Najeriya na da nasaba da abinda ke faruwa duniya sannan sauran ƙasashe na fama da irin su.

Masu cewa da wuya APC ta lashe zaɓe mai zuwa, basu san abinda suke cewa ba gabaɗaƴa.

Haka suka ce a 2019 APC ba zata ci zaɓe ba, saboda halin da ƙasar ke ciki, amma lokaci ya nuna cewa sun yi kuskure.

Abu mai muhimmanci shine abinda ke addabar ƙasar nan yana da nasaba da abinda ke faruwa a duniya. Gabaɗaya duniya na fama da rikici da hauhawar farashi.

Amurka na fama da hauhawar farashin da ba a taɓa gani ba a cikin shekara 40, haka ƙasar Ghana, Nijar da sauran makwabtan mu. Dole mu lura da abinda ke faruwa a duniya kafin sukar abinda ya zama gama gari a duniya. Matsalar da muke da ita tafi ƙarfin magancewar ƙasa ɗaya.

Ya shawarci ƴan Najeriya

Masari yace ko wane ɗan ƙasa nada rawar da zai taka wurin taimakawa gwamnatoci shawo kan matsalolin dake addabar ƙasar nan.

Ina kallon wannan a matsayin abu mai wucewa akan hanyar mu ta samun cigaba

Tun kafuwar Najeriya ba a taɓa samun ingantaccen shugaba irin shugaba Buhari ba -Gwamna Masari

A wani labarin na daban kuma, Gwamna Masari yace Najeriya bata taɓa samun nagartaccen shugaba kamar Buhari ba.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyana cewa tun lokacin da aka haɗe Najeriya a 1914, ƙasar bata taɓa samun ingantacciyar gwamnati da shugaban ƙasa irin shugaba Buhari ba.

Gwamnan ya faɗi haka ne ranar Asabar a Katsina yayin wani gangami wanda masu amfana da shirin gwamnatin tarayya na ‘Social Investment Programme’ (NSIP), na jihar su ka shirya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe